Tirkashi: Jim kadan bayan daura aurensu amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa bashi da mazakuta

Tirkashi: Jim kadan bayan daura aurensu amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa bashi da mazakuta

- Wani labari da wani mutumi ya wallafa a shafinsa na Twitter ya jawo kace nace sosai a shafukan sada zumunta

- Mutumin ya wallafa labarin yadda wata mata ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa bashi da mazakuta

- Wannan labari dai ya jawo kace nace matuka a shafukan sada zumunta inda wasu mutane ke gani bai kamata ya dinga tonawa mutane asiri haka ba

Wani dan Najeriya mai suna Chinedu Adikwu ya kawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ya wallafa labarin wata mata, wacce ta gano cewa mijinta bashi da mazakuta.

Mutumin ya wallafa labarin nashi a shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa mijin bashi da mazakuta, amma matar ta gano hakan ne bayan sun shiga daki da niyyar kwanciya.

KU KARANTA: An kuma: An kai wa fitaccen dan wasan Barcelona Lionel Messi hari a wani gidan rawa

Ga abinda mutumin ya wallafa:

"Wata mata ta rabu da wani dan uwana da yake zaune a kauye, bayan ta gano cewa bashi da mazakuta. Kuma tun farko an haifeshi babu mazakuta ne dama. An roke ta akan ta bari dan uwanshi ya kwanta da ita ko zasu samu 'ya'ya tare.

"'Yan mata ku tabbatar kun bincika kun tabbatar da mazajen da zaku aura basu da matsala kafin ku amince ku aure su."

Mutane da yawa masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi ta mayar da martani akan wannan labari da Chinedu ya wallafa, inda suka dinga bayyana labarin a matsayin rashin cancanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel