Allah daya gari ban-ban: Wata kabila da matansu suke yin zina da bakin su a matsayin hanyar karramawa

Allah daya gari ban-ban: Wata kabila da matansu suke yin zina da bakin su a matsayin hanyar karramawa

- Kabilar Himba kabila ce mai dumbin tarihi, sun kasance makiyaya, inda suke zaune a yankin Namibia na nahiyar Afirka

- Kabilr basu da aiki idan ba mata su fita tatsar nonon shanu ba, sannan su lura da yara, yayin da mazajensu zasu fita farauta na tsawon wasu kwanaki

- Wata babbar al'adarsu ita ce, al'adar da idan bako yaje gidajensu, miji zai dauki matarsa ya kai masa ita ya kwanta da ita a matsayin hanyar karramawa

A can yankin Kunene da Omusati dake arewacin Namibia, akwai wasu mutane manoma da makiyaya masu kabilar Ovahimba da Ovazimba.

Al'adace a wajensu mata su dinga fita kullum suna tatsar nono a jikin shanaye, sannan kuma su dinga lura da yara kanana, yayin da mazajensu kuma zasu tafi farauta, a lokuta da dama suna dadewa basu dawo ba.

Mutanen da yawansu ya kai sama da 50,000, kabilar Himba suna auren mataye da yawa, inda kuma suke aurar da 'yan matansu ga mazajen da suka zaba musu da sun kai minzalin balaga.

Sun cigaba da yin da yawa daga cikin al'adunsu duk kuwa da yanayin zuwan wayewar kai na turawa da kuma sukar da suke samu.

KU KARANTA: Hotuna: An hako gawar Sarki Namarudu da matarsa a kasar Iraqi, an same su sanye da gwala-gwalai na naira biliyan 12

Daya daga cikin al'adun nasu shine, mace ba ta da zabi a wajen yanke hukunci, kowanne abu ne ya taso sai ta nemi shawarar mijinta.

A yadda jaridar Guardian ta bayyana, "Idan bako ya je gidajensu, to mai gidan dolene ya nuna karramawa ta hanyar bashi matarsa ya kwana da ita, inda shi kuma mijin zai nemi wani daki ya kwanta idan akwai, idan kuma babu wani daki, mijin zai kwana a waje."

Wata al'adar da kabilar Himba suke yi har yanzu ita ce, haramtawa kansu yin wanka, maimakon su dinga yin wanka, matansu suna yin turare ne da hayaki sannan su saka wani jan abu a jikinsu. Suna saka wannan jan abu ne saboda sun yadda cewa ja na nufin "Duniya da Jini". Yanayin launin fatarsu shine yasa suka zamanto daban, kuma suna sanyawa kansu wannan jan abu ne saboda ya kare su daga yanayin zafin sahara da rana sannan kuma ya kare su daga cizon kwari.

Bayan haka kuma kabilar Himba basa yin bulaguro, koda yaushe suna garinsu, hakanne ya sa suka fita daban da sauran kabilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel