Yadda wani tsoho ya sha da kyar bayan an kama shi 'zigidir' a dakin matar aure

Yadda wani tsoho ya sha da kyar bayan an kama shi 'zigidir' a dakin matar aure

Wani dattijo a cocin Christ Apostolic (CAC) mai suna Elder Kwasi Agbo ya kusa rasa mazakutarsa bayan mazauna garin Akim Akwatia da ke Yankin Gabashin Ghana sunyi yunkurin datse masa mazakutar bayan kama shi zundir yana kokarin yin zina da matar aure da dakin mijin ta.

'Yan sandan garin sun tabbatarwa gidan rediyon Onua FM cewa a ranar Alhamis an kama Elder Agbo a ranar Lititin 22 ga watan Yuli amma an bayar da belinsa yayin da ake cigaba da bincike.

Wani mazaunin Akim Akwatia mai suna Yaw Aboagye wanda ya maganta kan lamarin a kafar rediyo ta Onua FM a shirin Yen Sempa a ranar Alhamis ya ce dattijon ya kyallara idonsa kan wata matar aure mai yara biyu da ba a bayyana sunanta ba kuma ya ce yana son ta.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

Matar da shaidawa dattijon cewa ya yi hakuri saboda tana da aure saboda haka ba za ta iya soyaya da shi ba amma Elder Agbo ya cigaba da matsa mata.

A cewar Yaw Aboagye, matar da gaji da fitinar dattijon sai ta fadawa mijinta abinda ke faruwa inda ya bukaci ta cewa dattijon ta amince tana son sa kuma ta gayyace shi gidan mijin ta.

Matar ta shaidawa Elder Agbo cewa ya zo gidanta su hadu a soye saboda mijinta ya yi tafiya.

Elder Agbo ya amsa gayyatar kuma suka kebe a daki har ya yi zigidir kwatsam sai mijin matar ya fito daga inda ya ke boye ya yi masa ihun kwarto kuma ya tara masa al'umma suka yi masa dukkan tsiya.

Bayan sun lalasa shi sosai sai suka yanke shawarar datse masa azzakari amma kafin su kai ga aikata hakan sai jami'an 'yan sanda suka iso wurin suka kwace shi da kyar.

A halin yanzu dai babu tabbas ko za a gurfanar da Elder Agbo a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel