Tirkashi: An gano wata mata tana shan fitsarin karenta, inda ta bayyana cewa yana maganin cutuka da dama

Tirkashi: An gano wata mata tana shan fitsarin karenta, inda ta bayyana cewa yana maganin cutuka da dama

- An nuno wata mata tana shan fitsarin karenta, inda ta bayyana cewa yana maganin cututtuka da yawa

- Ta bayyana cewa shan fitsarin karen ne yake sawa jikinta yana kara kyau da annuri

- Ta bayyana cewa fitsarin kare na da sinadarai da dama a cikinshi, sannan kuma yana maganin cutar daji

Wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wata mata take shan fitsarin karenta, inda ta bayyana cewa yanayi mata maganin kuraje.

Matar wacce take 'yar kasar Amurka mai suna Lynn Lew, an nuno ta lokacin da take shan fitsarin karen, inda ta bayyana cewa yana kara fuskarta haske da annuri.

A cikin bidiyon matar ta kuma sanar da cewa shan fitsarin karen yana maganin cutar daji.

ta ce: "Mutane da yawa suna yawan tambayana mai yasa kullum nake kara kyau, yadda kuma kwalliya ta take kara fito dani."

KU KARANTA: To fah: Babban burina a rayuwa shine na ganni a dakin mijina - Jaruma Teema Yola

Matar an nunota ta rike kofi a kusa da karenta, inda ta cika kofin da fitsarin karen.

Ta kara da cewa: "Sai da ta fara shan fitsarin karenta, sannan ta fara samun lafiya, kuma duka kurajen dake fuskarta sun warke.

"Fitsarin kare yana da sinadarin Vitamin A, Vitamin E da kuma sauran sinadarai a tattare dashi, kuma yana yin maganin cutar daji sosai."

An fara shan fitsarin mutane dana dabbobi ne dai a matsayin gwaji, kuma an fara gabatar da gwajin a kasar Rome, Greece da kasar Egypt.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel