Zakzaky: Dole ta sa mu ke fita mu na zanga-zanga Inji Ibrahim Musa

Zakzaky: Dole ta sa mu ke fita mu na zanga-zanga Inji Ibrahim Musa

Shugaban da ke kula da harkar yada labarai a kafofin zamani na kungiyar ‘Yan shi’a na IMN, Ibrahim Musa, ya yi hira da jaridar Daily Trust inda ya bayyana abubuwan da su ka shafii tafiyarsu.

Malam Ibrahim Musa ya nuna cewa babu laifin kowa sai shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen tsare babban Malaminsu watau Ibrahim Zakzaky da a ka yi na tsawon shekara da shekaru.

“Mun yi amanna cewa an shirya shari’ar babban kotun Kaduna ne domin gwamnati ta cigaba da garkame Malam yayin da ya ke fama da rashin lafiya. Ba a tashi shiga kotu ba sai bayan shekaru 3.”

Ibrahim Musa ya yi wannan magana inda ya kara da jefawa gwamnatin kasar tambaya da cewa “Meyasa gwamnati ta shafe shekaru uku bayan kisan gillar da a ka yi a Zaria kafin a soma shari’a a gaban kuliya?”

Musa wanda jagora ne na wani bangare na ‘yan shi’an Najeriya a karkashin lemar IMN ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta na yi wa umarnin kotu karon-tsaye don haka dole su ke ta faman zanga-zanga.

KU KARANTA: An ba Gwamnan Katsina shawarwarin yadda zai yi maganin rashin tsaro

“Ba mu yi kotu bore, zanga-zanga kurum mu ke yi duk rana ta Allah a Abuja saboda a saki Sheikh Zakzaky da Maidakinsa. Abin da mu ke so gwamnati ta yi, shi ne kawai ta ba Zakzaky da Matarsa ‘yancinsu”

Musa ya kuma bayyana cewa babu wani fito-na-fito da su ke yi da hukuma domin kuwa jami’an tsaro ne su ke far masu, da nufin ganin bayansu, yayin da su kuwa ba su dauke da wani makami.

A game da maganar yin zaman sulhu, Ibrahim Musa ya ke cewa ba su yi watsi da yiwuwar hakan ba. “Mu koma tarihi, an yi irin wannan a 1998 lokacin da Sani Abacha ya nemi ganin bayan Zakzaky.”

Jagoran na IMN ya ke cewa: “Mun zauna an tattauna, kuma an saki Zakzaky a lokacin da Janar Abdulsalami ya hau kan mulki.” Har yanzu ma dai IMN ta ce ana irin wannan tattaunawa da wata kasar waje.

Kungiyar ta Shi’a ta ji dadin yadda majalisa ta fara sa baki a kan takkadamar da su ke samu da jami’an tsaro. Kawo yanzu dai gwamnatin Najeriya ta ce sam ba za ta taba sakin Sheikh Ibrahim Zakzaky ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel