Sabbin ministoci: Guragu, makafi sun koka kan yadda Buhari ya mayar dasu saniyar ware

Sabbin ministoci: Guragu, makafi sun koka kan yadda Buhari ya mayar dasu saniyar ware

Masu bukatu na musamman, wadanda aka fi sani da nakasassu sun bayyana damuwarsa ga yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar dasu saniyar ware wajen nada sabbin ministocin gwamnatinsa.

Rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito wata kungiya mai zaman kanta mai suna cibiyar yan kasa masu bukatu na musamman ta bayyana haka yayin ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Arzikin kasa: An kasafta naira biliyan 762 tsakanin jahohi, kananan hukumomi da gwamnatin tarayya

Shugaban kungiyar, David Anyaele ne ya bayyana haka, inda yace hakan zai kawo koma baya ga al’ummar nakasassun Najeriya, ya kara da cewa hakan ya saba ma kashi na 6 na sashi na 29 na dokokin haramta nuna wariya ga masu bukatu na musamman na shekarar 2018.

“Muna kokawa kan rashin sanya nakasassu cikin mutane 43 da shugaban kasa ya aika ma majalisa da zai nadasu mukaman ministoci a gwamnatinsa, muna kira ga shugaban kasa ya dabbaka kashi na 7 na sashi na 31 na kundin dokokin yaki da nuna wariya ga nakasassu don kafa hukumar kula da nakasassu, tare da kira gareshi ya nada akalla ministoci 3 nakasassu a gwamnatinsa.” Inji shi.

Haka zalika shugaban kungiyar ya nemi shugabannin majalisun dokokin Najeriya su nada nakasassu a matsayin hadimansu don cike gurbin kashi 5 na ma’aikatansu kamar yadda dokokin yaki da nuna wariya ga nakasassu suka tanada.

Ita dai wannan kungiya ta kware wajen kulawa da hakkokin nakasassu, kulawa da walwalarsu tare da kokarin kwato mussu yancinsu a duk inda aka zaluncesu, ta hanyar wayar musu da kai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel