An yi dariya matuka yayin tantance zababbiyar minista daga jihar Kogi a majalisar dattawa

An yi dariya matuka yayin tantance zababbiyar minista daga jihar Kogi a majalisar dattawa

Sautin dariya tare da amso amo na kyalkyala ya mamaye zauren majalisar dattawa ta Najeriya a ranar Alhamis 25 ga watan Yuli yayin tantance zababbiyar minista daga jihar Kogi, Ramatu Tijjani Aliyu.

Wannan lamari mai yanayi da wasan kwaikwayo ya gudana a yayin da shugaba maras rinjaye Sanata Enyinnay Abaribe na jam'iyyar PDP, ya shigar da butakar a kawo karkashen yiwa Ramatu tambayoyi yayin tantancewa duba da kasancewarta mace sakamakon sanayyar da aka yiwa mata ta masu rauni.

Daya daga cikin jagorori a majalisar, Yahaya Abdullahi na jam'iyyar APC mai wakilcin jihar Kebbi, yayin goyon bayan bukatar da Sanata Abaribe ya shigar cikin harshen turanci, ya misalta Ramatu a matsayin mace mai kwazon aiki da tsayuwa wajen sauke nauyi. Ya yi amfani da jumlar turanci ta 'Dutiful lady'.

Fitar wannan jumla daga bakin Sanata Yahaya ke da wuya, ya sanya Sanatoci suka tuntsure da dariya domin a tunanin su ya yi amfanin da jumlar 'Beautiful lady' ma'ana mace mai kyau sabanin 'Dutiful lady' da ta fito daga bakin sa.

KARANTA KUMA: Ministoci: Majalisar dattawa ta tantance Aliyu, Shehuri, Magashi da wasu zababbu hudu

An yi dariya ta kusan minti biyar a yayin da Sanata Yahaya bai gushe ba wajen maimaita furucin da ya yi na misalta Ramatu a matsayin 'dutiful lady' wato mace mai kwazo domin tabbatar da matsayar sa da kuma gudun kaucewa mummunar fahimtar da sanatocin suka yi masa ta yabawa da kyawunta.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne majalisar dattawan kasar nan ta fara tantance jerin zababbun ministoci 43 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sunayen su bayan fiye da kwanaki 50 da karbar rantsuwa ta sabuwar gwamnatin sa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel