Kada ka zama kanwar-lasa a kan sha'anin 'Yan shi'a - JIBWIS ta shawarci Buhari

Kada ka zama kanwar-lasa a kan sha'anin 'Yan shi'a - JIBWIS ta shawarci Buhari

Kungiyar Jama'atu Izalitil Bid'ah Wa Ikamatis Sunnah JIBWIS, ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauka duk wasu matakai mafi dacewa wajen magance tarzomar da 'yan shi'a ke haddasawa a kasar nan.

Kungiyar JIBWIS ta shawarci Buhari a kan kada ya sake ya zamto kanwar-lasa wajen daukar matakai da za su magance munanan hare-hare da zangar-zangar 'yan shi'a ke haifarwa wajen tayar da zaune tsaye a kan jami'an tsaro da kuma sauran al'ummar Najeriya wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Shawarar JIBWIS na zuwa ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Yulin 2019, cikin wata sanarwa daga bakin jagoran ta, Sheikh Sani Yahaya Jingir, da ya gabatar yayin ganawa da manema labarai a ofishin sa dake birnin Jos na jihar Filato.

Sheikh Jingir ya jaddada cewa, kasancewar su kungiyar musulmi, ba za su zuba idanu a kan yadda al'amura ke neman tabarbarewa cikin kasar nan ba tare da tofa albarkacin baki ba da kuma bayar da gudunmuwa gwargwadon iko.

Ya gargadi majalisar dattawa a kan kada ta kuskura tantance duk wanda ta samu da nasaba cikin jerin zababbun ministocin Buhari ta kusa ko nesa ko kuma alakar goyon bayan masu akidar shi'a da sauran kungiyoyi masu neman rabuwar kai a kasar nan.

Cikin kalaminsa, "mun fahimci cewa cikin zababbun ministocin Buhari akwai mai goyon bayan akidar shi'ada ko kuma goyon bayan masu neman kawo rabuwar kai a kasar nan. Kada majalisar dattawa ta kuskura ta tabbatar da ire-iren su a matsayin jagorori a kasar nan."

"Abin takaici ne a samu cewa akwai wadanda ke daukar makamai domin yakar 'yan sanda tare da yunkurin kai hari majalisar tarayyar Najeriya. Baya ga hakan su na ikirarin neman samun damar kashe 'ya'yan shugaban kasa Buhari ko kuma shi a karan kansa yayin da suka samu babbar dama."

"Mu na fatan shugaban kasa Buhari ba zai ragawa wannan kungiya ba wajen daukar tsauraran matakai ta hanyar umartar hukumomin tsaro da su zage dantse wajen magance ta'addancin masu goyon bayan akidar shi'a."

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel