Kudi a kashe su ta hanya mai kyau: An sayar da takalmin da yafi kowanne tsada a duniya kan kudi naira miliyan 157

Kudi a kashe su ta hanya mai kyau: An sayar da takalmin da yafi kowanne tsada a duniya kan kudi naira miliyan 157

- An sayar da wani takalmi wanda yafi kowanne tsada a duniya, akan kudi naira miliyan dari da hamsin da bakwai

- Takalmin wanda wani tsohon dan wasa ya ciyo shi a wajen gasa a shekarar 1972 ya yiwa sauran takalma 'yan uwanshi zarra

- An bayyana cewa kamfanin Nike ne yayi takalmin, wanda a yanzu ya wuce sauran takalma irinsu Adidas da Air Jordan tsada

Wani takalmi na kamfanin Nike yayi kasuwa, yayin da aka sayar da shi akan kudi dala 437,500, kimanin naira miliyan dari da hamsin da bakwai da dubu dari biyar (N157,500,000) kenan a kudin Najeriya.

Takalman wadanda aka yi su tun a shekarar 1972, wanda mutumin da ya samar da kamfanin Bill Bowerman ya zana su, ana tunanin cewa kudin takalmin ba zai wuce dala 160 ba, amma kuma sai aka bayyana cewa shine takalmin da yafi kowanne tsada da aka sayar a birnin na New York.

KU KARANTA: Soja marmari daga nesa: Babu wata bindiga da zata iya kashe ni a duniyar nan - Bidiyon wani matsafin soja

Wani hamshakin mai kudi dan kasar Canada, Miles Nadal wanda ya sayi irin takalman guda 99 a wajen sayarwar, ya bayyana cewa zai sanya takalman ne a wajen wani ajiye kayan tarihinsa dake birnin Toronto, mai suna 'Dare to Dream Automobile Museum'.

Ba a buga irin wannan takalma da yawa ba, kuma duka an sayar dasu a ranar Talatar nan. Amma kuma wanda yafi kowanne tsada a cikinsun wani tsohon dan wasane ya ciwo shi a gasa a shekarun baya da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel