Yan Najeriya na kashe naira biliyan 434 wajen shigo da madara – CBN

Yan Najeriya na kashe naira biliyan 434 wajen shigo da madara – CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa nan bada jimawa gwamnatin Najeriya za ta haramta shigo da madara zuwa Najeriya daga kasashen waje, inji rahoton jaridar Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwamna Emefiele yana bayyana cewa Najeriya na kshe sama da dala biliyan 1.2, kimanin naira biliyan 434 kenan a duk shekara wajen shigo da madara daga wasu kasashen duniya.

KU KARANTA: Gwamnan Kano ya biya bashin N2,000,000,000 da ake bin daliban Kano a jami’ar Sudan

A cewar Emefiele: “Muna da shanu a Najeriya, kuma idan aka killace shanun nan ana kiwatasu ba tare da sun fita yawo ba, ana basu ruwa ana basu abinci, tsaf zasu iya samar da irin madaran da muke bukata mai inganci.

“Amma idan sakesu sakaka suna yawo, shine ke basu daman cinye duk abinda suka gani a hanya, kuma wannan ne ke kawo tashe tashen hankula, a yanzu haka mun fara tattaunawa da wasu manyan kamfanonin madara a Legas domin su dawo Najeriya su zuba jari ta yadda zasu fara samar da madara a Najeriya.” Inji shi.

Sai dai gwamnan ya kara da cewa a yanzu haka wasu kamfanoni sun fara rungumar wannan tsarin, kamar kamfanin Friesland Campina dake masu Peak milk sun kirkiro wani tsarin sayan madara a wajen makiyaya yan Najeriya guda 3,500 a cibiyoyi 5.

A yayin wata ziyara da kamfanin ta kai ma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a shekarar 2018, inda suka bayyana cewa zasu zuba hannun jarin Yuro miliyan 23, tare da dayen shanu daga makiyaya 500, sai dai kamfanin ta koka kan rashin tallafi daga gwamnati.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel