Zan ba Matasa kujerar Minista a Gwamnati – Buhari a lokacin zabe

Zan ba Matasa kujerar Minista a Gwamnati – Buhari a lokacin zabe

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jama’an Najeriya alkawarin cewa zai tafi da Matasa idan ya zarce. Shugaban kasar ya nuna cewa zai ba masu jini a jika kujerar Minista a gwamnatinsa.

A cikin makon nan ne kuwa shugaban kasar ya aika sunayen Ministoci domin majalisa ta tantance su. Wannan ya sa matasa su ka tado wancan tsohuwar maganar da shugaban kasar ya yi.

A cikin mutane 43 da shugaba Muhammadu Buhari ya zaba Ministoci, ba a samu wani Matashi ko guda daya ba. Wannan ya ci karo da alkawarin da shugaban kasar ya yi wa mutane da bakinsa.

A cikin sababbin Ministocin har da mai shekara 73 a Duniya, Sabo Na Nono. Kusan ‘Dan Autan cikin Ministocin bai gaza shekaru 45 da haihuwa ba. Hakan na nufin babu wani Matashi a cikinsu.

KU KARANTA: Jerin Matan da Shugaban kasa Buhari ya rabawa kujerun Minista

A lokacin da Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar APC da Tony Nwoye ya jagoranta har fadar shugaban kasa a lokacin kamfe, Buhari ya yi alkawarin zai tafi da su.

Shugaban kasa Buhari ya fada masu cewa idan har a ka sake zabensa a wani karo, Matasa za su samu kujeru na Minista da kuma shugabannin hukumomi da ma’aikatu na gwamnatin tarayya.

Wannan ya sa Tony Nwoye da mutanensa su ka yi wa shugaban kasar wanda shi ne ‘dan takarar jam’iyyar APC mai mulki alkawarin goyon baya da kuri’u akalla miliyan 20 a zaben na 2019.

A karshe, Nwoye da kwamitinsa ba su kai ga cika wannan alkawari da su dauka ba. Haka zalika, shugaban kasar bai zabi wani Matashin da zai rike masa ko da Minista guda a wannan karo ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel