Jerin sunayen sabbin bankuna guda 3 da bankin CBN ta amince da kafawa

Jerin sunayen sabbin bankuna guda 3 da bankin CBN ta amince da kafawa

Babban bankin Najeriya, CBN, ta sanar da karin bankuna guda uku a Najeriya bayan ta baiwa sababbin bankunan guda uku lasisin fara aiki, kamar yadda ta bayyana a shafinta na yanar gizo, inji rahoton jaridar The Cables.

A shafin nata, babban bankin ta bayyana adadin bankunan Najeriya ya karu daga 21 zuwa 23, sai kuma wani sabon bankin Musulunci guda daya da zai dinga aiki ba tare da kudin ruwa ba.

KU KARANTA; Kan yan majalisa ya rabu game da matakin daya kamata gwamnati ta dauka a kan yan Shia

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bankunan guda uku sun hada da Titan Trust Bank Limited, Globus Bank Limited da kuma bankin Musulunci na TAJ Bankin Limited, wanda ya kawo adadin bankunan Musulunci a Najeriya zuwa biyu har da bankin Jaiz.

A watan Yunin data gabata ne gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa bankin na duba yiwuwar kara adadin jarin bankunan Najeriya domin tabbatar da suna da isassun kudi a kasa a kowanni lokaci.

Wannan mataki na kara yawan jarin bankuna shine zai tabbatar da tsaron kudaden masu zuwa hannayen jari a bankunan da kuma abokan mu’amalarsu, idan za’a tuna a shekarar 2004 ne CBN ta kara adadin jarin bankunan daga naira biliyan 2 zuwa naira biliyan 25.

Wanda hakan yasa bankunan Najeriya da dama suka gaza, wanda dole tasa aka samu hadakan bankuna da dama domin su hada wannan kudi, yayin da wasu da dama kuma suka rushe sakamakon ba zasu iya hada wannan kudi ba, wannan tasa bankunan Najeriya suka ragu daga 89 zuwa 24.

Daga bisani kuma an samu wasu bankunan da suka dinga hadaka, wani ya hadiye wani har sai da adadin bankuna ya kara saukowa zuwa 21.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel