Kishi kumallon mata: Ta yiwa saurayinta dukan tsiya a cikin jirgi saboda ya kalli wata budurwa - (Bidiyo)

Kishi kumallon mata: Ta yiwa saurayinta dukan tsiya a cikin jirgi saboda ya kalli wata budurwa - (Bidiyo)

- Wani bidiyo da ya dinga yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wata mata ta dinga dukan saurayinta saboda kawai ya kalli wata mata dake gefen shi

- Lamarin ya kawo rikici sosai a cikin jirgin inda matar taki sauraron kowa a cikin jirgin ta dinga zage-zage da dukan saurayin nata

- A karshe dai an sauke matar da saurayin daga cikin jirgin, inda ta nuna masa cewa a wajen jirgin ma bai tsira ba, domin kuwa hannu ta saka ta dinga naushinsa

Wata mata ta wuce gona da iri akan saurayinta yayin da suke cikin jirgi, inda ta fara dukan sa saboda ya kalli wata mata a gefensa.

A wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta, ya nuna matar 'yar kasar Amurka tana ta zagin saurayin nata, wanda take kiran shi da 'Memo'. Abin ya wuce yadda ake tunani, domin kuwa matar ta hana ma'aikatan jirgin raba rikicin a cikin jirgin, wanda zai tashi daga birnin Miami zuwa Los Angeles.

KU KARANTA: Tonon silili: An kama wani ma'aikacin banki yana kokarin yin zina da wata budurwa a cikin banki

Matar tayi ta zagin saurayin nata, inda take zargin shi da cewa yana kallon wata mata daban.

Ma'aikatan sun yiwa matar magana akan irin zage-zagen da take yi a cikin jirgin, inda suka bayyana mata cewa akwai yara da bai kamata su dinga jin irin wadannan kalmomin daga bakinta ba, sai ta ha da ma'aikatan jirgin da yaran duka tayi musu kudin goro.

A karshe dai an sauke matar da saurayin nata daga jirgin, inda ta cigaba da dukan shi da hannu.

Ga dai bidiyon abinda ya faru a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel