Gadar miliyan N700 da Kwankwaso ya gina a Kano ta tsage

Gadar miliyan N700 da Kwankwaso ya gina a Kano ta tsage

Gadar kasa ta unguwar Gadon Kaya da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya gina a kan miliyan N700 ta tsage.

Ruftawar da gadar ta yi ya jefa masu ababen hawa a cikin wahala saboda rufe hanyar da hukuma ta yi.

Gadar, wacce ke sada masu ababen hawa da jami'ar Bayero da ke Kano, ta rufta ne ranar Lahadi.

A Cewar wani rahoto da gwamnatin jihar Kano ta fitar ranar Talata, saman gadar ya tsage tare da ruftawa sakamakon ruwan sama da aka sha a garin Kano a daren ranar Lahadi, lamarin da ya jawo aka hana ababen hawa bi ta hanyar gaba daya.

Gadar miliyan N700 da Kwankwaso ya gina a Kano ta tsage
Gadar miliyan N700 da Kwankwaso ya gina a Kano ta tsage
Asali: Facebook

An rufe hatta hannu daya na gadar da bai rufta ba, wanda zai kai masu ababen hawa zuwa Kofar Famfo.

DUBA WANNAN: Dubun dan fashi da ke buya a cikin kabari ta cika

Kwankwaso ya gina gadar ne a kan miliyan N700 a zangon mulkinsa na biyu daga 2011 zuwa 2015.

Kamfanin gine-gine na Rocard ne ya yi kwangilar aikin gadar wacce Kwana sa ya saka wa suna 'Gadar Prince Abubakar Audu'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel