Kowa ya debo da zafi bakinsa: 'Yan coci sun yiwa Faston su dan karen duka

Kowa ya debo da zafi bakinsa: 'Yan coci sun yiwa Faston su dan karen duka

- Wasu fusatattun mambobin wata coci a kasar Kenya sun afka cikin cocinsu sun hau Faston su da duka, bayan wani lamari da ya faru da bai yi musu dadi ba

- Lamarin ya samo asali ne bayan kan mambobin cocin ya rabu biyu, inda wasu suke goyon bayan shugaban cocin, wasu kuma suke kalubalantar shi, inda har abin ya kai su ga shiga kotu

- Rikicin dai ya zo karshe ne bayan zuwan jami'an 'yan sanda cocin, inda suka harba barkonon tsohuwa kowa ya bar wajen

An samu tashin hankali a cocin Central Seventh Day Adventist (SDA) dake Nairobi, Kenya, ranar 20 ga watan Yulin nan, bayan wasu fusatattun mambobin cocin sun shiga cikin cocin sun rufe Faston mai suna Jean Pierre Maywa da duka.

Rikcin ya samo asali ne a lokacin da wasu mambobin cocin da suke goyon bayan Faston suka taru domin kawo hanyar da zasu raba kan cocin biyu. Bayan rikicin mambobin cocin dama kotu tayi watsi da wata kara da mambobin cocin suka kai gabanta, inda suka kalubalanci shugabancin cocin.

KU KARANTA: To fah: Ni talaka ne ku taimaka ku saki mahaifiyata - Samson Siasia ya roki wanda suka yi garkuwa da mahaifiyarsa

A wajen neman masalahar da aka zauna, an fara cacar baki, inda har ta kai ga rikici ya balle a tsakaninsu. A wani bidiyo da aka sanya a shafin sada zumunta na Twitter, an gano wasu mambobin cocin suna ihu yayin da wasu kuma suka tashi suke kare shugaban cocin.

An kawo karshen taron ne bayan jami'an 'yan sanda sun karaso wajen sun jefa barkonon tsohuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel