Kwadayi mabudin wahala: Wani dan sanda ya tsorata bayan ya gano cewar karuwar da ya dauko ba mace bace katon gardi ne

Kwadayi mabudin wahala: Wani dan sanda ya tsorata bayan ya gano cewar karuwar da ya dauko ba mace bace katon gardi ne

Wani abu da zamu iya kira da abin dariya ya faru, bayan wani dan sanda da ke aiki a Abuja ya kira wata karuwa da nufin ta taya shi kwana, a karshe dai ya kare da mamaki bayan ya gano abinda ba shi yayi tsammani ba

Labarin da ya same mu ya bayyana wani dan sanda da yake aiki a yankin Kubwa dake Abuja ya dauki wata karuwa daga wani kulob dake cikin gari da nufin yin lalata da ita.

Amma wani abu da ya daure mishi kai shine yadda ya gano cewar karuwar da ya dauko ba mace bace katon gardin namiji ne yayi shigar mata ya fito domin ya wanki gara.

A wani bidiyo da yanzu yake yawo a shafukan sada zumunta na, an nuno saurayin yana cire abubuwan da ya sanya a jikinshi yayi ciko dasu.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: An cafke wasu samari guda uku da suka yiwa wasu tsofaffin ma'aurata gunduwa-gunduwa da adda

A cewar shi yana amfani da wannan kayan mata ne da dare kawai sannan kuma ya da rana sai yayi shigar maza ya fita harkokinsa.

Daya daga cikin masu binciken shi yayi masa alkawarin zai bashi aiki wanda zai samu kudi masu tsoka idan har ya daina wannan harkar.

Haka kuma Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa mata masu yawan karuwanci na kara karuwa a kasar Italy, inda aka bayyana cewa akwai kimanin karuwai 'yan Najeriya dubu goma a kasar ta Italy.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel