Kisan Musulmi: A karon farko kasar Amurka ta nuna rashin jin dadinta da kisan kiyashin da ake wa Musulmi a Myanmar

Kisan Musulmi: A karon farko kasar Amurka ta nuna rashin jin dadinta da kisan kiyashin da ake wa Musulmi a Myanmar

- Kasar Amurka ta sanya takunkumin hana manyan shugabannin kasar guda hudu tare da iyalansu shiga kasar ta Amurka

- Amurka ta dauki wannan matakin ne bayan zargin da tayi na kisan kiyashi da manyan sojojin suke yiwa Musulmi a kasar Myanmar

- Musulmi suna cikin wani hali a kasar ta Myanmar bayan irin barazanar da suke fuskanta daga wajen sojojin na kasar Myanmar

Kasar Amurka ta bayyana cewa ta sanya takunkumi akan wasu manyan shugabannin sojoji na kasar Myanmar, bayan ta zargesu da take hakkin dan adam wurin kashe Musulmi 'yan kabilar Rohingya.

Sojojin da takunkumin ya shafa sun hada da babban hafsan hukumar sojin kasar, Min Aung Hlaing.

Ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya bayyana cewa shugabannin sojojin guda hudu ne da ke da alhakin kisan kiyashin a kasar ta Myanmar, a lokacin da ya bayyana cewa sunyi yunkurin kawar da Musulmin kasar.

KU KARANTA: Ran maza ya baci: Ku ajiye makamanku ko kuma ku hadu da balbalin bala'i - Bulama Biu ya gargadi 'yan Boko Haram

Wannan doka da kasar ta Amurka ta sanya akan wadannan sojoji guda hudu na nufin daga yanzu babu wani daga cikinsu ko cikin iyalansu da zai kara zuwa kasar Amurka.

Ministan kasar ta Amurka ya bayyana cewa, wannan mataki da kasar ta dauka shine na farko da wata kasa a fadin duniyar nan ta dauka akan wadannan manyan shugabannin sojoji na Burma.

Shekaru biyu da suka gabata dubban al'ummar Musulmi sun dinga hijira daga kasar ta Rohingya zuwa kasar Bangladesh, saboda tsattsauran matakin da hukumar sojin kasar Myanmar ta dauka na kisan gilla da kuma gallaza musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel