Babbar magana: Ya yiwa kakar matarshi dukan kawo wuka saboda ta kasa rarrashin jaririyarshi ta daina kuka

Babbar magana: Ya yiwa kakar matarshi dukan kawo wuka saboda ta kasa rarrashin jaririyarshi ta daina kuka

- Wata dattijuwa ta shiga wani ibtila'i yayin da mijin jikarta yayi mata dukan kawo wuka

- Mijin jikartan ya zane ta ne saboda ya shigo ya tarar da jaririyar da aka haifa masa 'yar wata takwas tana kuka ita kuma ta kasa rarrashinta

- An gano cewa tsohuwar ce take daukar nauyin dukkanin dawainiyar gidan nasu, saboda mutumin baya yin aikin fari bare na baki

Wata mata 'yar kasar Malaysia mai shekaru 69 ta samu wasu manyan raunika a fuskarta, bayan anyi zargin mijin jikarta yayi mata dukan tsiya saboda ta kasa rarrashin jaririyarshi ta daina kuka.

Shugaban 'yan sanda na garin Jasin, Arshad Abu ya ce matar ta samu ciwuka da dama a tsakiyar kanta da kuma kujewa a kusa da idanuwanta a lokacin da lamarin ya faru da misalin karfe 6 na safiyar Litinin dinnan da ta gabata.

Ya ce yanzu haka tsohuwar tana karbar magani a asibitin Jasin, kuma za a kaita asibitin Melaka don cigaba da duba lafiyar idonta, ya kara da cewa akwai yiwuwar tana iya rasa idanuwanta saboda dukan da mutumin yayi mata.

KU KARANTA: Tirkashi: Ni dan gidan Dagaci ne, saboda haka babu wanda ya kaini asali a Kano - Ganduje

"Bincike ya nuna cewa kafin lamarin ya faru, jikar tsohuwar tana zaune a wani daki, inda ita kuma jaririyar ke daki daya da tsohuwar tana kuka. Mutumin na shigowa sai ya fara zagin tsohuwar akan cewa bata kula da jaririyar, inda ya mangareta har sai da ta fadi kasa. Jim kadan bayan ya gama yi mata dukan tsiya, ya dauki matarsa da 'yarsa suka gudu," in ji shi.

Mutumin wanda bashi da aikin yi, sannan suna zaune da tsohuwar tun lokacin da suka yi aure. Tsohuwar ita ce take daukar nauyin duka dawainiyyar su, inda take yin aikin dafa abinci a wata makarantar Islamiyya.

'Yan sanda sun kama mai laifin dan shekara 24 a Bachang da misalin 11 na daren ranar da ya aikata laifin, sai dai kuma an gano cewa ya sha kwaya ne.

Dama can dai mutumin tsohon mai laifi ne, sau biyu ana kama shi da laifin tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel