Jerin kamfanoni 34 da gwamnati ta baiwa kwangilar hakar danyen man fetir a Najeriya

Jerin kamfanoni 34 da gwamnati ta baiwa kwangilar hakar danyen man fetir a Najeriya

A wani sabon tsari na bani gishiri in baka manda, gwamnatin Najeriya ta bayyana sunayen kamfanoni 34 da suka samu kwangilar hakar danyen mai daga Najeriya, tare da baiwa Najeriya tataccen man fetir da suka shigo dashi.

Legit.ng ta ruwaito hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC ce, ta sanar da sunayen kamfanonin a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, inda tace wannan sabon tsari zai samar da isashshen man fetir a Najeriya, musamman tunda matatun man kasar basa aiki.

KU KARANTA: Rugujewar gidan sama a Jos: An tabbatar da mutuwar mutane 8

Matatun man Najeriya guda hudu nada daman samar da iyaka gangan mai guda 445,000 ne a duk rana, amma kuma tsawon shekara da shekaru kenan basa aiki yadda ya kamata.

Hukumar NNPC ta raba kamfanonin da zasu yi aikin kwangilar gida 15 ne, inda a ranar Litinin, 15 ga watan Yuli ne NNPC ta mika ma kamfanonin takardun kwangilar, yayin da taron rattafa hannu a kan kwangilar zai biyo baya.

Ga jerin kamfanonin da suka samu gwaggwaban kanwagilar kamar haka:

BP/Aym Shafa

Vitol/Varo

Trafigura/AA Rano

MRS

Oando/Cepsa

Bono/Akleen/Amazon/Eterna

Eyrie/Masters/Cassiva/Asean Group

Mercuria/Barbedos/Petrogas/Rainoil

UTM/Levene/Matrix/Petra Atlantic

TOTSA

Duke Oil

Sahara

Gunvor/Maikifi

Litasco /Brittania-U

Mocoh/Mocoh Nigeria

Masana a masana’antar man fetir sun jinjina ma kamfanin NNPC bisa wannan tsari, wanda suka ce tun a shekarar 2016 ne sabon shugaban NNPC, Mele Kyari ya kikiro wannan tsari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel