Rugujewar gidan sama a Jos: An tabbatar da mutuwar mutane 8

Rugujewar gidan sama a Jos: An tabbatar da mutuwar mutane 8

Wani sabon rahoto yaa tabbatar da mutuwar mutane 8 da hatsarin rushewar gidan sama mai hawa 2 ta rutsa dasu a garin Jos, tare da tabbatar da mutane 4 da suka samu rauni daban daban.

Hatsarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Yuli a Layin Butcher, unguwar Dilimi, cikin karamar hukumar jos ta Arewa, kamar yadda jaridar Legit.ng ta tabbatar inda ta ruwaito gidan mallakin Alhaji Rufai Kabiru ne.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi garkuwa da babban jami’in gwamnatin Zamfara, sun kashe 1

Da misalin karfe 5 na yammacin Litinin aka sanar da rushewar gidan sama mai hawa 2 dake titin Butcher a karamar hukumar Jos ta Arewa, nan da aka kaddamar da aikin ceto, inda aka ceto mutane 7 ba tare da samu rauni ba, mutane uku sun mutu sai kuma wasu mutum 3 da suka samu rauni.

Sai dai an dakatar da aikin ceto da misalin karfe 11 na dare saboda karancin kayan aiki da zasu haskaka wajen da kuma gajiya da ma’aikatan suka yi, amma da sanyin safiyar Talata, misalin karfe 7 na safe tuni ma’aikatan suka taru suka koma bakin.

Daga cikin ma’aikatan da suke gudanar da aikin ceto akwai jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, hukumar baga agajin gaggawa ta jahar Filato SEMA, hukumar bada agaji ta duniya, Red Cross, jami’an tsaro da kuma jama’an gari.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito zuwa yammacin Litinin an gani gawarwakin mutane uku, zuwa karfe 10 aka gano na wata mata mai ciki da gawar Alhaji Kabiru Nalele mahaifin maigidan kenan, yayin da da misalin karfe 8 na safiyar Talata aka gano gawarwakin wasu mutane uku.

Kaakakin Yansandan Filato, DSP Terna Tyopev yace tuni suka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na jahar Filato da kuma asibitin koyarwa na jami’ar Bingham domin samun kulawar data dace.

Daga karshe ya bayyana cewa suna cigaba da aikin ceto ta hanyar dage baraguzan ginin domin tabbatar da babu wanda aka bari a cikin baraguzan, haka zalika Yansanda sun killace inda lamarin ya auku.

Sai dai kaakaki Terna bai bayyana musabbabi aukuwar hatsarin ba, amma a cikin gidan akwai shagon sayar da magani da kuma gidan wanka da ba haya, kuma jama’a sun bada gudunmuwa sosai wajen ceto mutanen da rugujewar ginin ta rutsa dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel