Babban bankin Najeriya ta bayar da lasisi ga wani sabon bankin Musulunci

Babban bankin Najeriya ta bayar da lasisi ga wani sabon bankin Musulunci

Wani rahoton da muka samu da dumi dumi daga jaridar Iwitness ta tabbatar da cewa babban bankin Najeriya, CBN ta bayar da lasisin fara aiki ga wani sabon bankin Musulunci a Najeriya, mai suna TAJ Bank Limited.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban bankin ta sanar da amincewarta da fara aikin wannan sabon bankin Musuluncin ta cika ne cikin wata wasika data aika mata a ranar Litinin, 15 ga watan Yuli, sakamakon gamsuwa da tayi da cikan dukkan sharuddan data gindaya mata.

KU KARANTA: Gwamna Bala Mohammed ya yi ma shugaban ma’aikatan Bauchi ritaya

Sai dai CBN ta iyakance ayyukan Bankin TAJ a iya yankunan Arewa maso yammaci da kuma Arewa maso gabashin Najeriya, amma ta bata daman ta samar da babban ofishinta a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan cigaba da aka samu a harkar cinikayyar kasuwanci irin na Musulunci ya kawo adadin bankunan Musulunci a Najeriya zuwa biyu, bayan samuwar bankin Musulunci na Jaiz tun a shekarar 2011.

Idan za’a tun a shekarar 2003 aka fara haihuwar Jaiz a matsayin cibiyar hada hada cinikayya irin na Musulunci da bata ta’ammali da riba, yayin da a shekarar 2011 CBN ta batalasisin fara aiki a iya Arewacin Najeriya, don haka ta zama bankin Musulunci na farko a Najeriya.

Bankin Musulunci na JAIZ bai fara aiki ba sai a ranar 6 ga watan Janairu na shekarar 2012, inda bayan samun karbuwa suka nemi izinin CBN ta basu daman su fadada ayyukansu zuwa sauran sassan Najeriya, wanda a shekarar 2016 CBN ta bata lasisin aiki a dukkanin sassan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel