An tono gawar wasu 'yan mata uku a gidan wani mutum da suka hadu a 'Facebook'

An tono gawar wasu 'yan mata uku a gidan wani mutum da suka hadu a 'Facebook'

'Yan sanda a kasar Afrika ta kudu sun tono gawar wasu 'yammata uku a farfajiyar gidan wani mutum a Mpumalanga, wanda ya amsa cewa ya kashe su ne bayan ya sadu da su.

Kakakin rundunar 'yan sanda, Kanal Mtsholi Bhembe, ya ce an fara tono gawar wata mata a gidan mutumin da ke yankin Masoyi kimanin sati uku da suka gabata bayan an bayyana bacewar ta tun a watan Mayu.

"Mutumin da ake zargi da kashe ta ya bayyana cewa sun hadu a dandalin sada zumunta na Facebook. Ya kara da cewa ya sadu da matar kuma ya sallameta ta tafi.

"Ya kara da cewa washegari sai matar ta dawo ta na neman ya kara mata wasu kudin. A nan ne suka tafka mahawara har ta kai ga matar ta mare shi, shi kuma ya naushe har ta fadi kasa, kan ta ya bugu, a cewarsa," a cewar Kanal Bhembe.

Bhembe ya kara da cewa mutumin ya shaida musu cewa bai fahimci cewa matar ta mutu ba sai bayan wani lokaci.

Mutumin mai shekaru 25 ya ce ya tube kayan matar tare da binne ta bayan ya gane cewa ta mutu.

An tono gawar mace ta biyu ranar Juma'a, yayin da ta ukun aka tono ta a ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Kotu ta daure malamar makaranta bayan samunta da laifin yin lalata da dalibi mai shekaru 13

Ya binne gawar biyu daga cikin 'yammatan a cikin gidansa. Bhembe ya ce an samu gawar 'yan matan a kusa da juna, amma ya daure gawar daya daga cikinsu da waya.

"Ya shaida mana cewa ya sadu da dukkan 'yan matan amma sun samu sabani a kan kudi. Ya yi zargin cewa wasu daga cikinsu sun yi masa barazanar cewa zasu shigar da karar shi a kotu bisa cewa ya yi musu fyade, shi kuma jin hakan ya rikita shi.

"A cewarsa, ya kashe mata hudu kenan daga shekarar 2018 zuwa 2019. Mun samu ragowar kasusuwan wasu matan bayan ya nuna mana inda ya binne su," a cewar Bhembe.

Ana sa ran za a gurfanar da mutumin, wanda yanzu haka ke hannun 'yan sanda, a gaban kotu ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel