Abin bakin ciki: Yadda wasu 'yammata 2 suka hada daki da wani da surukin babansu don yin garkuwa da shi

Abin bakin ciki: Yadda wasu 'yammata 2 suka hada daki da wani da surukin babansu don yin garkuwa da shi

- 'Ya'yan wani dattijo mai shekaru 88 sun hada baki da wani mai niyyar zama surukinsa wajen yin garkuwa da mahaifinsu

- Mai niyyar zama surukin dattijon ya ce zai yi amfani da kudin fansar da zasu samu domin biyan kudin sadakin diyar dattijon

- Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Frank Mbah, ya ce masu laifin kwararru ne a bangaren garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa

A ranar Litinin ne kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Frank Mba, ya yi bajakolin asu masu laifi da suka hada da wani mutum da ya kashe wata tsohuwar 'yar bautar kasa bayan ya yi mata fyade da wasu mutane biyu, 'ya'yan wani dattijo mai shekaru 88, da suka hada baki da wani wajen yin garkuwa da mahaifinsu.

Da yake bayyana wa manema labarai yadda abin ya faru, Mba ya bayyana cewa, "wani abun takaici ya faru, inda wasu 'ya'yan dattijo mai shekaru 88 suka hada baki da wani mai niyyar zama surukinsa tare da yin garkuwa da shi.

"Chinaza, mai shirin angonce wa da Emmanuel, ta hada baki da dan uwanta, Emeka, tare da sace mahaifinsu domin su karbi kudin fansa."

DUBA WANNAN: Babu wannan zancen: NNPC ta karyata labarin karin kudin farashin mai

A cewar Mba, Emmanuel ya shaida wa rundunar 'yan sanda cewa zai yi amfani da kudin fansar da zasu samu domin biyan sadakin diyar dattijon.

Mba ya kara da cewa, "jami'an rundunar yaki da garkuwa da mutane ne suka kama masu laifin a ranar 29 ga watan Yuni bayan samun wasu bayanan sirri a kan al'amuransu.

"Masu laifin, wadanda dama kwararru ne a harkar yin garkuwa da mutane domin karbar kudn fansa a yankin Mbaise da ke jihar Imo, sun amsa laifinsu tare da bawa rundunar 'yan sanda muhimman bayanai. Kazalika sun bayyana irin rawar da suka taka a garkuwa da mutane daban-daban a yankin da suka fito."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel