Atiku ya koka kan yawan bashin da Buhari ya ciyo ma Najeriya a shekara 4

Atiku ya koka kan yawan bashin da Buhari ya ciyo ma Najeriya a shekara 4

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana damuwarsa da dimbin bashin kudade da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take ciyo ma Najeriya.

Atiku ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Paul Ibe, inda yace bashi ya yi ma Najeriya katutu sakamakon yadda shugaba Buhari ke antayo ma kasar dimbin basussukan da za’a dade ana biyansu tsawon shekara da shekaru.

KU KARANTA: Garkame Zakzaky: Sheikh Ahmad Gumi ya kai ma Bola Tinubu ziyara don shawo kan Buhari

Atiku bayyana cewa gwamnatin PDP ta bar ma Najeriya bashin naira tiriliyan 12 a shekaru 16 da tayi tana mulki, amma zuwa Buhari cikin shekaru hudu ya ninka wannan adadi, ya kara da cewa daga watan Disambar 2018 zuwa Maris na 2019 Buhari ya ciyo ma Najeriya bashin naira biliyan 560.

“Abin haushin ma shine yawancin abubuwan da suka yi da kudaden kamar su Tradermoni sun kirkiresu ne saboda siyasa kawai domin su yaudari yan Najeriya su basu kuri’u a zaben shugaban kasa daya gabata, kuma zabe na wucewa suka dakatar da aikin.

“Mun kasa gane yadda za ace duk da bakin talaucin da Najeriya ke fama dashi, amma gwamnati ke ciyo mana dimbin bashi, bugu da kari cin hanci da rashawa na karuwa a kasar, kamar yadda Amnesty International ta tabbatar.” Inji shi.

Daga karshe Atiku ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada su mayar da Najeriya mabaraciyar kasa, kuma su tabbata sun dauki matakin rage ciyo basussuka kafin hakan ya karya tattalin arzikin kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel