Gaba kura baya sayaki: Yan ‘kato da gora’ sun kashe mutane 17 a jahar Katsina

Gaba kura baya sayaki: Yan ‘kato da gora’ sun kashe mutane 17 a jahar Katsina

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta sanar da kama wasu yan kato-da-gora guda 4 da laifin kashe wasu mutane fararen hula su 17 a kauyen Kwatawa dake karamar hukumar Safana ta jahar Katsina.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutanen da Yansanda suka kama sun hada da; Abdullahi Abubakar mai shekaru 30, Lawal Abubakar dan shekara 28, Abdulsalam Sani mai shekara 35 da kuma Salisu Isah dan shekara 38.

KU KARANTA: Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 5 da zai nada muhimman mukamai

A ranar Talata, 9 ga watan Yuli ne matasan sa kai suk kai farmaki zuwa wani rugar Fulani ne dake kauyen Kwatawa da nufin daukan fansan abokansu guda uku da suke zargin fulanin da kashewa, inda suka kashe mutane 17.

A cewar yan bangan, a ranar 7 ga watan Yuni ne yan Fulani yan bindiga dauke bindigogin AK-47 suka afka ma abokansu yayin da suke gona a karamar hukumar Safana inda suka kashe mutum uku da suka hada da Ashiru Mansir, Muddaha Mandir da Jabiru Mansir.

Zuwa yanzu dai rundunar Yansandan jahar Katsina ta kammala bincike akan yan kato da goran, kuma ta gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci hukuncin laifin da suka aikata kamar yadda sashi na 97 da 221 na kundin hukunta manyan laifuka suka tanadar.

Alkalin kotun dake sauraron karar, Fadila Dikko ta umarci a daure mata matasan 4 a gidan yari zuwa ranar 22 ga watan Agusta don cigaba da shari’ar, kamar yadda dansanda mai kara, Sajan Lawal Bello, ya nema.

A wani labari kuma, wasu gungun yan bindiga sun afka wani gidan da ake kulawa da marayu da gajiyayyu, Great Saints Orphanage dake garin Issele-Uku cikin karamar hukumar Aniocha ta Arewa na jahar Delta.

Rahoton jaridar New Nigerian ta bayyana cewa yan bindigan sun lalata wani sashi na gidan tare da barnata wasu motoci dake ajiye a farfajiyar gidan marayun, kamar yadda mai gidan, Emeka Ezeagbor ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel