Ikon Allah ne kadai ya sanya na samu mukamin sakataren gwamnatin Tarayya - Boss Mustapha

Ikon Allah ne kadai ya sanya na samu mukamin sakataren gwamnatin Tarayya - Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha, ya ce shakka babu akwai wadanda suka sha gaban sa ta fuskar cancantar mukamakin kujerar da yake kai a yanzu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a 5, ga watan Yulin 2019, ya sake sabunta nadin mukamin sakataren gwamnatin Tarayya da kuma Abba Kyari, a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin sa.

Da yake gabatar da jawabai a ranar Litinin da ta gabata, Boss Mustapha ya bayar da shaidar yadda ya samu kwarewa mai zurfin gaske yayin sauke nauyin mukamin sa na kujerar sakataren gwamnatin Tarayyar kasar nan.

Ya yi godiya ga Mai Kowa Mai Kowa da kuma shugaban kasa Buhari da ya sanya aminci da kuma dogaro a gare sa.

KARANTA KUMA: Saurayi dan shekara 14 ya shiga hannu da laifin fyade a kasar Jamus

Babban sakataren na kasa ya bayar da tabbacin sa ga al'ummar kasar nan a kan cewa zai jajirce wajen gudanar da aiki tukuru yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa fiye da ya yi a wa'adin sa na farko.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel