‘Yan Majalisa na shirin tafiya hutu Buhari bai aika sababbin Ministoci ba

‘Yan Majalisa na shirin tafiya hutu Buhari bai aika sababbin Ministoci ba

Sanatocin Najeriya za su fara hutun su a cikin wannan watan muddin har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza kawowa majalisar sunayen wadanda ya ke so su zama Ministocinsa.

Kamar yadda mu ka ji, a daidai wannan lokaci, Sanatocin kasar ba su kagara shugaba Buhari ya aiko masu da jerin wadanda ya ke so a tantance a matsayin Ministocin gwamnatin tarayya ba.

Haka kuma ‘yan majalisar ba za su fasa zuwa hutunsu da zarar lokaci ya yi ba saboda kurum su na jiran shugaban kasa ya aiko da sunayen Ministocin da a ke ta jira tun bayan da APC ta ci zabe ba.

Majiyar ta mu ta bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawa sun yi Allah-wadai da irin nawar shugaba Buhari wanda ya lashe zabe tun a farkon bana, kuma ya koma cikin ofis a karshen Mayu.

KU KARANTA: Buhari ya rattaba kan kasafin kudin babban birnin tarayya

Sanatoci sun nuna cewa rashin gabatar da sunayen Ministoci ba zai sa su fasa zuwa hutu a Ranar 26 ga Watan Yuli ba. Wani Sanatan ya ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa da su yi wannan babban aiki.

Kamar yadda ‘dan majalisar ya nuna zai yi kyau shugaban kasa ya aiko masu sunayen Ministocinsa a tantancesu kafin a tafi dogon hutu domin a samu gwamnati mai-ci ta soma aiki Najeriya.

Wani Sanatan Kudu ya bayyanawa ‘yan jarida cewa za su yi aikinsu ne a natse ba tare da garaje ba. Wata Macen Sanata kuwa cewa ta yi bai kamata a yi watanni kafin a nada Ministoci ba.

Mai magana a madadin Sanatocin kasar, Adedayo Adeyeye, ya bayyana cewa:

“Idan shugaban kasa ya kawo sunayen kafin mu tafi hutu, za mu duba lamarin. Haka kuma idan a ka kawo sunayen Ministocin a lokacin mu na cikin hutu, babu mamaki a tado ‘yan majalisa bakin aiki saboda yi wa kasa aiki.”

Sanata Adedayo Adeyeye ya bayyana cewa a shirye majalisa ta ke da ta zauna kan batun tantance Ministocin. Adeyeye ya ce aikin shugaban kasa ne ya kawo takarda, su kuma na su ne su tantance.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel