Kurunkus: Magana ta canja akan zuwan mawakiya Nicki Minaj Saudiyya - Sheikh Kabir Gombe

Kurunkus: Magana ta canja akan zuwan mawakiya Nicki Minaj Saudiyya - Sheikh Kabir Gombe

Babban shehin malamin na Musulunci, kuma sakataren kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Kabir Gombe yayi tsokaci akan batun zuwan mawakiyar Turani, Niki Minaj kasar Saudiyya.

Kabiru Gombe ya nuna takaicinsa akan yadda wasu mutane ke yiwa al’umman kasa mai tsarki kudin goro akan wannan lamari da ya kunno kai.

Shehin malamin ya bayyana cewa ba wai sarakunan kasa mai tsarki bane ke shigo da wadannan bidi’a kasar ba, a’a yace wasu yan tsirarrun Larabawa ne ko kokarin shigo da bidi’a a kasar.

Ya kara da cewa tuni dai sarakunan kasar suka yi wata zaman gaggawa domin kauracema zuwan mawakiyar kasar.

Shafin Alfijir Hausa ta ruwaito inda malamin ke cewa: “Sarakunan saudiyya, tare da masu fada aji na 'kasar na saudiyya, sunyi wata zaman gaggawa, domin 'kauracema wannan babban bidi'ar da wadan su tsirarun Matasan Larabawa ke 'kokarin shigowa da shi 'Kasar saudiyya.

“Ina mamakin yanda naji, na gani da ido na, ta yadda jama'a suke ta musayen yawu da junar su, tare da tayar da jijiyon wuyan su a banza, duk sun hana Kansu sukuni, don kawai sunci karo da labarin gaiyatar mawakiyar turawa zuwa 'kasa mai tsarki.

“Abin ban kunya shine! Ga al'umnar Musulmin duniya, da zaran anyi kacibir da wata 'Yar labari, wacce ta shafi saudiyya, musamnan dangane da Al'amuran da suka shafi jin dadin rayuwa, sai kaji jama'a nata kumfan baki, suna tsinema 'kasa mai tsarki.

“Hakan bai tsaya nan ba, sheikh kabiru gombe ya 'kara da cewa! Bari na sanya kulki na sare duk wata harshen da take aibanta 'kasa mai tsarki, saudiyya 'kasa ce, wacce akwai Matasa masu jini a jika na zamani, kuma gasu gayu ne! Tom ire-iren su' wadannan matasanne suke shirya irin wadanna bidi'ar a 'kasa mai tsarki, bawai sarakunan 'Kasar ba ne, don yanzu haka ma an dakatar da wannan al'amari na gaiyatar mawakiyar zuwa cashewa a bikin tunawa da zagowar haiwuwar wani matashin balarabe a 'Kasar saudiyya.

KU KARANTA KUMA: Shikenan ta faru ta kare: Saudiyya ta gayyaci Nikci Minaj ta bude musu taron waka da Bismillah

“Babu shakka jama'a na bani mamaki, don kawai mawakiya za ta zo 'kasar saudiyya sai ya zamana jama'a suyi ma duk cikan Al'ummar dake saudiyya kudin goro wurin aibanta su! Ya Ku jama'a wai bakusan a saudiyya akwai bayin Allah Ba ne ? Wadanda suke kwance! A kaburburan su, Amma sai jama'a saboda da 'kiyaiyya da Allah Sai kuyi ta la'antar 'Kasar baki dayan ta ? To wallahi tallahi mu kiyaye, ku mu shiga taitayin mu, don 'Kasar saudiyya ba 'kasa bace Wanda zai zama Abun muzantawa a idon musulmi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel