Wata sabuwa: An kashe mutane tara 'yan Najeriya a harin da aka kai kasar Libya
- Kimanin mutane tara aka kashe a wani hari da aka kai kasar Libya ranar Talatar nan da ta gabata
- Rahotanni sun bayyana cewa yawancin wadanda aka kashe din mata ne da yara kanana
- Har zuwa yanzu dai ba a gano ainahin wadanda suka kai harin ba
Kimanin 'yan Najeriya tara ne a cikin mutane 53 da aka kashe a wani hari da aka kai kan wani sansani da ake tsare 'yan cirani a kasar Libya, duniya ta yi Allah wadai da wannan hari.
A binciken farko da jami'an kasar Najeriya suka yi a yayin da suka ziyarci sansanin a yankin Tajoura, sun bayyana cewa 'yan Najeriya tara ne suka rasa rayukan su a wannan hari.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa harin da aka kai cikin daren Talatar nan da ta gabata a kasar Libya, wanda yayi sanadiyyar mutuwar 'yan cirani 53, zai iya zama yaki.
KU KARANTA: Abinda ya faru a shari'ar Abba Gida Gida da Ganduje yau a kotu
Gwamnatin kasar Libya wacce take samun goyon bayan manyan kasashe na duniya da abokin gabarta Khalifa Haftar suna zargin junansu da kai harin.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana cewa ma'aikatan Najeriya dake kasar sun gano mata guda uku, namiji daya, da wani karamin yaro da yake koyon tafiya, sai kuma wani yaro mai shekaru 10 a duniya.
Ma'aikatar ta ce tana jiran taga jerin sunayen mutanen dake gurin kafin lamarin ya faru, saboda hakan ne zai bata damar gane cewa akwai wasu 'yan Najeriya da harin ya ritsa dasu ko babu.
Haka kuma ma'aikatar ta nemi a gabatar da cikakken bincike domin gano wadanda suka yi wannan aika-aika a kuma hukunta su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng