Zamfara: Shinkafi ya roki EFCC ta bincike Yari a kan badakalar biliyan N251

Zamfara: Shinkafi ya roki EFCC ta bincike Yari a kan badakalar biliyan N251

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Zamfa a karkashin inuwar jam'iyyar APGA, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, ya bukaci mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) na kasa, Ibrahim Magu, da ya fara binciken tsohuwar gwamnatin jihar Zamfara da Alhaji Abdulaziz Yari ya jagoranta.

A cikin takardar korafin da ya aika wa EFCC, shinkafi ya yi zargin cewa tsohon gwamna Yari ya yi almubazzaranci da biliyan N251 mallakin jihar Zamfara.

Ya zargi tsohon gwamnan ta tafka badakala da kuma wofantar da dukiyar jihar Zamafara a tsawon shekaru takwas da ya yi ya na mulkin jihar.

Da ya ke bayar da ba'asin yadda gwamnatin Yari ta tafka badakala da kudin jihar, Shinkafi ya bayyana cewa Yari ya bar bashin N151,190,477,572.02 na aiyukan da ba a karasa ba.

Ya ce tsohon gwamnan ya yanki N1,431,645,303.99 a matsayin kudaden gidaje daga albashin ma'aikatan jihar Zamfara daga shekarar 2016 zuwa 2019.

DUBA WANNAN: Kotu: Atiku ya gabatar da akwatinan zabe 50 daga jihohin arewa 4 a matsayin shaida

Sannan ya kara da cewa gwamnatin Yari ta bar tulin bashi a ma'aikatar ilimi da kudaden jarrabawa da na wasu makarantu da ke wajen jihar da yawansu ya kai N2,812,172.155.

Shinkafi ya kara da cewa daga cikin biliyan biyu da gwamnatin Yari ta ware domin biyan bashin kudin garatuti na ma'aikatan da suka yi ritaya, tsofin manyan sakatarori kawai gwamnatin ta biya miliyan N400 tare da bayyana cewa babu wanda ya san yadda tsohon gwamnan ya yi da biliyan daya da miliyan 600.

"A saboda haka mu na kira ga hukumar EFCC da ta binciki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, a kan almubazarranci, wasoso, karkatar wa da yin almubazzaranci da kudaden jihar Zamfara da yawansu ya kai biliyan N251 kamar yadda shugaban kwamitin mika mulki karkashin tsohon mataimakin gwamna, Malam Ibrahim Wakala, ya yi zargi," a cewar Shinkafi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng