Ana shirin kai wadanda suka daura aure a Facebook kotu a Kano

Ana shirin kai wadanda suka daura aure a Facebook kotu a Kano

Rahotanni sun kawo cewa hukumar Hisbah a jihar Kano na neman wasu ma’aurata bayan da suka yi aure a shafin sadarwa na Facebook.

A hira da yayi da shafin BBC, Angon mai suna Sanusi Abdullahi dan shekara 29 ya bayyana cewa shi wasa kawai yake yi da yarinyar ba tare da sanin cewa karamar Magana zai zama babba ba.

Sanusi yace: "Tattaunawa muke yi a wani zauren Facebook da sauran mutane, kamar wasa sai yarinyar ta ce na aure ta ni kuma na ce to, bayan wani lokaci sai ta sake aiko min da sako ta ce ta samu wanda zai zama waliyin ta, ni ma sai abokina ya ce zai yi min waliyi.

"Sai muka amince da sadaki kan naira 20,000, daga nan sai abokina da waliyin nata suka gaya mana dukkan abin da ake bukata a aure."

Sanusi ya ce jim kadan da faruwar lamarin sai mutane suka fara yada zancen cewa ya yi aure daga nan sai ya kira yarinyar ya ce mata wannan auren fa kamar ya dauru, bari mu tambayi malaman musulunci saboda mutane na ta cewa auren ya tabbata.

Ya kara da cewa: "Da muka kira sai wasu suka ce ai aure ya dauru tun da akwai shaidu kuma na yi alkawarin biyan sadaki, amma da na tuntubi Sheik Ibrahim Daurawa, wani babban malami sai ya ce aure bai dauru ba tun da iyayen yarinya ba su sani ba.

"Ya ce yaya za a yi aure ba tare da sanin iyayen yarinya ba."

KU KARANTA KUMA: Ranar farko, Atiku da PDP sun gabatar da hujjoji 883 kan cewa anyi magudi a jiha daya kacal

Kakakin Hukumar Shari'a ta Kano, Sanusi Mohammed ya bayyana cewa tuni sun bai wa Hisbah umarnin kama matasan domin ya zama misali ga masu irin wannan auren wasa a kafafen sada zumunta.

Yace: "Abin da suka yi ya sabawa Musulunci, abu na gaba da za a yi bayan Hisbah ta kama su shi ne za akai su kotu daga nan kuma alkali zai yanke hukuncin da ya dace da su.

"Shari'a ta tanadi hukunci ga kowane irin laifi."

Sanusi ya ce tuni ya gudu daga gidansu saboda lamarin:"Na ji labarin cewa Hisbah na nema na don a kama ni amma ina tattaunawa da iyayena kan ko na kai kaina gare su.

"Amma abin da nake so mutane su gane shi ne abun da ya farun kuskure ne kuma na ba da hakuri.

"Ban taba shiga masallaci don halartar daurin aure ba a rayuwata don haka ban san yadda abin yake ba, kuma na yi alkawari ba zan sake aikata irin haka ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: