An tsayar da albashi da alawus din hadiman Buhari da Osinbajo

An tsayar da albashi da alawus din hadiman Buhari da Osinbajo

Rahotanni sun kawo cewa an tsayar da albashi da alawus din hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Kudaden wadanda aka dakatar sun hada da dukkanin wadanda wa’adin aikin su ya kare daga ranar 28 ga watan Mayu, 2019, kuma ba a sabonta musu takardar ci gaba da aiki tare da Shugaba Buhari ko Mataimakin nasa ba.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wadannan hadimai na cikin jidali, saboda babu wanda aka biya albashin watan Yuni, kuma an dakatar da dukkan alawus dinsu.

Sama da wata daya kenan tun bayan sake rantsar da Buhari karo na biyu, amma har yau bai sabonta nadin na su ba kuma bai kore su ya nada sabbi ba.

Buhari bai sallami ko daya daga cikin su ba, amma kuma ya bar su a kewaye da shi su na ci gaba da yi masa hidima shi da Osinbajo.

Wannan katankatana ta rashin sallamar hadiman shugaban kasa da kuma kin nada wasu, ta haifar da surutai a kasar nan, har lauyoyi na cewa haramun ne a tsarin dokar kasar nan a bar wadannan hadimai na ci gaba da aiki bayan wa’adin su ya cika a kan aiki.

Sama da hadimai 100 tare da iyalan su ne suka samu kan su cikin wannan hali, ciki har da manyan hadiman Buhari na yada labaai, Garba Shehu da Femi Adesina.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Hankalin mutane ya dugunzuma yayin da wani bututun mai ya tarwatse (bidiyo)

Wata majiya a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa hadimai uku ne kadai wannan lamari ba ta shafa ba.

Wadanda abin bai shafa ba sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapaha, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari da kuma Mataimakin sa, Adeola Ipaye wanda ke Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng