Abin kunya baya karewa a kasar nan: Can aka hango 'yan majalisar PDP suna bawa hammata iska a cikin dakin majalisa
- An hango 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar PDP suna bawa hammata iska a cikin dakin majalisa
- Hakan ya biyo bayan yadda kakakin majalisar wakilai na kasa ya bayyana Ndudi Elumuelu a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar, wanda ba shine 'yan jam'iyyar PDP suke so ba
- 'Yan majalisar wakilan jam'iyyar PDP sun bayyanawa kakakin majalisar cewa suna so ya bai wa wani dan majalisa dan asalin jihar Rivers mukamin sai kuma suka ga sabannin haka
Jiya Laraba ne aka hango Wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar PDP suna musayar naushi ga junansu, akan mukamin shugaban marasa rinjaye na majalisar.
Duk da dai jiya Laraban komai an fara shi cikin kwanciyar hankali. Amma daga baya komai ya rikice bayan da kakakin majalisar wakilan, Femi Gbajabiamila ya bayyana Ndudi Elunmelu a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan.
KU KARANTA: Kudi masu gidan rana: Jerin mutane 30 da suka fi kowa kudi a Najeriya da kamfanonin su
Hakan bai yiwa 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar PDP dadi ba, domin kuwa sun riga sun rubutawa kakakin majalisar cewa suna so ya bai wa Kingsley Chinda, dan majalisar wakilai daga jihar Rivers matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar.
A jiya ne dai kakakin majalisar wakilan ya bayyana sunan Ndudi Elumuelu a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar.
Ba wannan ne karo na farko da aka saba ganin 'yan majalisar suna bawa hammata iska a cikin dakin majalisar ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng