Yanzu Yanzu: Osinbajo ya shilla kasar Rwanda
Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bar babban birnin tarayya Abuja domin zuwa kasar Ruwanda.
Osinbajo zai wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a wurin taron bikin cikar kasar Rwanda shekaru 25 da samun 'yan ci wanda za a gudanar a ranar Alhamis 4 ga watan Yulin 2019.
Hakan na dauke ne cikin jawabin da hadiminsa na fannin kafafen yada labarai, Mr Laolu Akande ya fitar inda ya ce, " Farfesa Osinbajo zai hadu da sauran shugaban kasahen Afirka a wurin taron da ake sa ran gudanarwa a ranar Alhamis 4 ga watan Yuli a Kigali domin tuna kawo karshen kisar kare dangi da akayi a kasar a 1994.
DUBA WANNAN: Magajin Garin daura: 'Yan sanda sun kama wadanda suka yi garkuwa da shi, sun samu alburusai
"Wasu manyan jami'an gwamnati za su yi wa mataimakin shugaban kasar rakiya zuwa taron."
Ana sa ran zai dawo gida Najeriya a ranar Alhamis 4 ga watan Yulin 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng