An bayyana adadin mutanen da ke ta'ammuli da ganyen wiwi a Najeriya

An bayyana adadin mutanen da ke ta'ammuli da ganyen wiwi a Najeriya

Kungiyar sa ido kan miyagun kwayoyi da manyan laifuka na Majalisar Dinkin Duniya (UNODC) ta bayyana cewa akalla mutane miliyan 10 ne ke ta’ammali da ganyen wiwi a Najeriya.

UNODC ta sanar da hakan ne a wurin taron nemo hanyoyin magance illar ta'amulli da miyagun kwayoyi da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa ta'amulli da ganyen wiwi ya zama ruwan dare duba da cewa kimanin mutane miliyan 188 ke amfani da ita a duniya baki daya.

A cewar jami'in UNODC Oliver Stolpe, kungiyar ta gano hakan ne cikin wata binciken da tayi a 2018.

DUBA WANNAN: An bayyana aninin dalilin da yasa Sani Aliyu ya yi murabus daga NACA

A baya Legit.ng ta kawo muku cewa Hukumar yaki da fasa kwabri ta kama kullin tabar wiwi 1,682 wanda ya kai kudi Naira 25,290,000 boye a cikin gawa da wata babbar mota a kan iyakar Seme.

Kwantirola na bodar, Mohammad Garba ya bayyana cewa a ranar Talata aka shigo da haramtacciyar tabar ta kan iyakar.

Ya ce jami’an su sun tsayar da wata mota da ke dauke da gawa a bisa zargin cewa akwai wani abun da aka boye a gawar.

“Bayan da aka bincika sai jami’an mu suka gano kulli 55 na tabar wiwi a kalkashin akwatin da aka dauko gawar.”

“An kama mutane biyun da ke cikin motar nan take amma an kyalesu an tafi da gawar don a binne. Haka zalika, an boye kulli 1,582 a cikin wata mota, kanta, kirar Mitsubishi da aka lullube ta da ledar taliyar Indomie.

“An kuma kama kulli 45 na tabar wiwi a wurare daban daban wanda hakan ya bada adadin yawan tabar da aka kama ya zama 1,682."

“Mutane takwas din da aka kama za a tuhume su a kotu, Inji Garba.

Ya kara da cewa hukumar ba za tayi kasa a gwuiwa ba wajen yakin da fasa kwabrin da sauran laifuffukan da akeyi a tsakanin bodar kasannan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164