Allah ka raba mu da aikin dana sani: An wayi gari Muhammed ya kashe matarsa da 'ya'yansa guda 9, sannan ya kone gawarsu kurmus
- Jami'an 'yan sandan kasar Pakistan sun samu nasarar cafke wani mutumi mai suna Mohammed Ajmal
- An kama Mohammed Ajmal da laifin kashe matarsa, 'ya'yansa guda biyu da kuma 'yan uwan matarsa guda shida, wanda suka je har gida suka bude musu wuta
- Baban Ajmal da dan uwansa sune suka taya shi yin wannan aika-aika, inda yanzu haka Ajmal da baban nashi suke hannun hukuma, kuma an tafi farautar dan uwan nashi
Yau Talatar nan ne jami'an 'yan sanda na kasar Pakistan suka cafke wani mutumi da laifin kashe mutane tara, ciki hadda matarsa da 'ya'yansa, inda ya kone gawarwakinsu daga baya.
Wani jami'in dan sanda mai suna Imran Mahmood ya bayyana cewa Mohammed Ajmal, ya dawo garinsu na Multan dake birnin Punjab daga kasar Saudiyya kwanaki kadan da suka wuce, inda ya fara zargin matarsa tana lalata da wani.
Mahmood ya ce matar mutumin tana gidan iyayenta sai Ajmal shi da babansa da dan uwansa suka afka gidan suka bude musu wuta, hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane tara.
KU KARANTA: Tirkashi: Na sha kama mijina dumu-dumu yana zina da mata akan gadonmu na Sunnah
"Matar Ajmal, 'ya'yanshi guda biyu da kuma mutane shida na dangin matar tashi sune suka mutu.
"Daga baya mutanen sun sanyawa gidan wuta sun kone gawarwakin kurmus."
Jami'in dan sandan ya bayyana cewa yanzu haka sun kama Ajmal da babansa, sannan kuma suna iya bakin kokarinsu wurin ganin sun cafke dan uwansa da ya gudu.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar Pakistan ta ce a kowacce shekara mazaje na kashe daruruwan mataye saboda zargin suna yin lalata da wasu a kasar.
Hukumar 'yan sanda ta bada rahoton cewa kusan mutane 800, wanda suka hada da maza da mata wadanda aka dinga kaiwa hari saboda irin wannan zargi a shekarar 2018 a kasar ta Pakistan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng