Gwamna El-Rufai na shirin sanar da jerin sunayen sabbin kwamishinoninsa

Gwamna El-Rufai na shirin sanar da jerin sunayen sabbin kwamishinoninsa

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shirya tsaf domin gabatar da jerin sunayen sabon majalisarsa a gaban Majalisan dokokin jihar

- Wata majiya ta bayyana cewa El-Rufai zai gabatar da sunayen tsakanin yau Talata, 2 ga watan Yuli da kuma gobe Laraba, 3 ga watan Yuli

- Majiyar ta tattaro cewa majalisarsa za ta kunshi matasa da ya dade yana ba horo na musamman

Rahotanni sun kawo cewa Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya shirya tsaf domin gabatar da jerin sunayen sabon majalisarsa a gaban Majalisan dokokin jihar.

Wata majiya mai inganci a majalisar dokokin jihar ce ta tabbatar ma da jatidar Daily Trust daren jiya Litinin, 1 ga watan Yuli cewa suna sa ran samun jerin sunayen tsakanin yau Talata ko gobe Laraba.

A cewar majiyar wanda ya neMi a sakaya sunansa, yace sunayen sun hada da na matasa wadanda gwamnan ya ba horo a shekarun da suka gabata.

Majiyar ta kara dacewa daga abunda ya tattaro, bayan majalisar ta gama tantance sunayen, Gwamna El-Rufai zai tura su ma’aikatu da kuma mukamai a ofishin sa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi sabon nadi mai muhimmanci

“Ga dukkan alamu Kwamishinoni masu kwazo ne kawai za su dawo, yayinda wasu jami’ai za su zamo cikakkun kwamishinoni daga mukamin shugabanni a wasu hukumomi,” inji majiyar.

Ya kara da cewa a halin yanzu hukumomin tsaro suna aiki akan wasu daga cikin sunayen.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng