Allah Ya tseratar da Magajin garin Daura bayan shafe wata 2 a hannun barayi

Allah Ya tseratar da Magajin garin Daura bayan shafe wata 2 a hannun barayi

Allah Ya kubutar da magajin garin Daura, kuma surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Musa Umar Uba daga hannnun miyagun da suka yi garkuwa dashi tun kimanin watanni 2 da suka gabata.

Legit.ng ta ruwaito rahotanni daga garin Daura sun tabbatar da haka, inda suka bayyana cewa a ranar Talata, 2 ga watan Yuli ne Magajin Gari ya dawo gida, cikin koshin lafiya, bayan jajirtattun jami’an Yansanda sun kwatoshi.

KU KARANTA: Allah Ya tseratar da Magajin garin Daura bayan shafe wata 2 a hannun barayi

Allah Ya tseratar da Magajin garin Daura bayan shafe wata 2 a hannun barayi
Abba Kyari tare da Magaji
Asali: Facebook

Idan za’a tuna a ranar 1 ga watan Mayu ne wasu gungun yan bindiga guda hudu suka kai farmaki gidan Magajin garim Daura, inda suka yi awon gaba dashi yayin da yake zaune a kofar gidansa bayan sallar Magariba.

Bayanai sun bayyana akan yadda Yansanda na musamman na IRT dake karbar oda daga babban sufetan Yansandan Najeriya a karkashin jagorancin DCP Abba Kyari suka gudanar da aikin ceton Magajin Gari.

Abba Kyari da tawagarsa sun kaddamar da samame ne a gidan da yan bindigan ke rike da Magajin gari dake Samegu akan hanyar zuwa Madobi a cikin jahar Kano, anan aka dinga musayar wuta tsakanin Yansandan da miyagun.

Sai dai da yake Yansandan sun fi su kwarewa da sanin makaman aiki, da wuta yayi wuta sai miyagun suka ranta ana kare, da haka ne Yansandan suka ceto Magajin gari, suka mikashi zuwa gidan dake garin Daura bayan ya huta.

Yan uwa da abokan arzikin sun yi ta kwarara zuwa gidan don yin ido hudu dashi, kuma anyi sa’a ya isa gida cikin koshin lafiya, daga cikin wadanda suka fara isa gidan akwai Aminu Jamo, wani hamshakin dan kasuwa dan asalin garin Daura.

Shi dai magajin gari ya kasance kani ne ga mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, kuma tsohon kwanturola ne a hukumar hana fasa kauri ta kasa watau kwastam, haka zalika yana auren Hajiya Bilki, diyar babbar yayar shugaba Buhari, Hajiya Rakiya.

Bugu da kari, babban dogarin shugaban kasa Buhari, Kanal Muhammad Abubakar yana auren diyarsa Fatima.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng