Buhari ya nada Farfesa Sambo a matsayin sabon shugaban hukumar inshoran lafiya

Buhari ya nada Farfesa Sambo a matsayin sabon shugaban hukumar inshoran lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nada Farfrsa Mohammed Sambo a matsayin sabon shugaban hukumar inshoran lafiya ta kasa, NHIS, domin ya maye gurbin Farfesa Usman Yusuf da aka sallama daga aiki.

Legit.ng ta ruwaito wata sanar daga dake dauke da sa hannun daraktan watsa labaru na ma’aikatar kiwon lafiya, Boade Akinola ta bayyana cewa shugaba Buhari ya rusa majalisar gudanarwar hukumar ta NHIS.

KU KARANTA: Kasashen duniya sun zabi dan Najeriya shugaban kungiyar OPEC

Buhari ya nada sabon shugaban hukumar inshoran lafiya
Sambo
Asali: Facebook

Sanarwar tace “Biyo bayan shawarwari da kwamitin binciken kwakwaf mai zaman kansa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa ta bayar akan badakalar NHIS, shugaba Buhari ya amince da sallamar Farfesa Usman Yusuf a matsayin shugaban hukumar NHIS, sa’annan ya nada Farfesa Mohammed Sambo a matsayin sabon shugaban hukumar.

“Haka zalika shugaban kasa ya amince da rusa hukumar gudanarwar NHIS, sa’annan ya umarci babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya ya dauki ragamar tafiyar da hukumar kafin a nada sabbin shuwagabanninta.” Inji sanarwar.

A hannu guda kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dakta Chikwe Ihekweazu a matsayin babbar daraktan hukumar kula da cututtuka na Najeriya.

Idan za’a tuna tun a kwanakin baya ne tsohon ministan kiwon lafiya, Farfesa Isaac Adewole tare da hadin gwiwar yayan hukuar gudanarwar NHIS suka sanya ma tsohon shugaban hukumar, Farfesa Usman Yusuf tsama, wanda har ta kai ga sun dakatar dashi daga aiki, amma Buhari ya mayar dashi bakin aikinsa.

Sai dai a karo na biyu, hukumar gudanarwar ta sake dakatar dashi akan zarge zargen cin hanci da rashawa, yayin da shi kuma ya zargesu da kare manyan kamfanonin dake ci da gumin yan Najeriya, tun wannan dakatarwa ne dai bai sake komawa ofis ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng