Limamin Juma’a ya rabu da mukaminsa saboda bijire ma Sarkin Kano

Limamin Juma’a ya rabu da mukaminsa saboda bijire ma Sarkin Kano

A kokarinsa na tabbatar da ikonsa, da kuma mulkinsa, mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya tsige wani babban limamin masallacin juma’a a garin Kano tare da rabashi da mukaminsa.

Legit.ng ta ruwaito Sarki ya raba wannan limami mai suna Salihu Muhammad da mukaminsa ne sakamakon bijire ma umarnin mai martaba da yayi dangane da ganin jinjirin watan idi.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje yayi nadin sabbin mukamai masu muhimmanci guda 26

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa ba wannan bane karo na farko da Liman Salihu ke yi ma umarnin Sarki karan tsaye ba, inda ko a bara ma sai da ya yi ma Sarki irin wannan rashin biyayyar, dangane da ganin wata.

Wadanda suke da masaniya akan lamarin sun bayyana cewa shi liman Salihu baya ajiye Azumin watan Ramadana sai ya ga wata da kansa, koda kuwa fadar mai martaba Sarki ta tabbatar da ganin watan.

A wani labarin kuma har yanzu tana kasa tana dabo akan batun fasa masarautar Kano gida 5 da gwamnan jahar, Abdullahi Umar Ganduje yayi, kuma masarautar birnin Kano take jayayyada matakin.

Dukkanin bangorin sun ki tsagaita wuta, inda gwamnan yace ba zai yi amai ya lashe game da raba masarautar Kano zuwa gida 5 ba, yayin da ita kuma masarautar birnin Kano ta shigar da karar gwamnan a gaban kotu.

Idan za’a tuna manyan mutane, daga cikinsu har da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya sun shiga rikicin, inda suka nemi gwmanan da Sarkin da sulhunta tsakaninsu ba tare da an ji su ba, amma hakan ya ci tura.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng