Malami

Malami

Rahotanni sun kawo cewa ana zargin wani malamin addini a jihar Osun mai suna, Habeebulah Abdulrahman wanda aka fi sani da Al-Edewy da yiwa dalibarsa mai shekara 16 fyade.

Da yake martani, Abdulrahman ya bayyana wa majiyarmu ta Premium Times cewa yarinyar matarsa ce kuma cewa yana da ikon Tarawa da ita.

Anhaifi yarinyar a sjekarar 2003, ta kuma rasa mahaifinta tun tana yar karama amma sai tana zama da mahaifiyarta a Ede, wani gari a jihar Osun. Bata dade da kammala makarantar karamar sakandare ba

Bincike ya nuna cewa malamin a watan Janairu ya gayyaci yarinyar domin ta fara zuwa makarantar Islamiyarsa wanda bai da nisa da gidansu, domin koyon karatun Al-Qur’ani. Sai yarinyar ta fara da amincewar mahaifiyarta.

Sai dai kuma bayan dan lokaci kadan sai malamin ya nemi auranta yarinyar ta ki amincewa amma Abdulrahman ya ci gaba da nace mata har said a yayi mata fyade.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa yana ta bai wa yarinyar kyaututtuka da nufin jan hankalinta domin ta aure shi, amma da aka tunkare shi sai yayi ikirarin cewa yana tallafa mata ne domin ta kasance marainiya.

Yadda abun ya faru:

A ranar 18 ga watan Afrilu, malamin yayi tafiya zuwa Ilaro da ke jihar Ogun domin halartan wani taron wa’azi tare da yarinyar da kuma wasu dalibai maza biyu

Yayinda aka yiwa daliban maza biyu masauki a waje guda, Mista Abdulrahman ya sauka daki daya dashi da yarinyar yayi kokarin Tarawa da ita amma ta nemi doki sannan ta ja hankalin masu otel din, inji ta

Yarinyar tayi ikirarin cewa yayi mata fyade a wannan ranar.

A hanyarsu ta dawowa jihar Osun, malamin ya ziyarci yan uwansa a Abeokuta, inda ya sake yiwa matashiyar fyaade.

A cewar yarinyar, a Abeokuta, ya tara da ita ta karfin tuwo a baya idon daliban maza biuyu da yan uwansa

A halin da ake ciki bayan fyaden, yarinyar ta daina halartan makarantar Islamiyyan sannan iyayenta suka yi shiru kan lamarin har sai da dan uwanta da ke zama a wajen Osun ya samu labara a lokacin da ya ziyarci Ede a watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Farawa da Bismillah: Ma'aikatan wata jiha a kasar nan sun bada tabbacin fara karbar sabon albashi

A cewar mahaifiyar yarinyar, Misis Ibrahim, malamin ya fara duba kokarin yarinyar a makaranta, wanda hakan yasa take ganin kawai yana tausayin iyalin ne.

Sai da suka sakankance dashi ya aikata masu ta’asa, ta kuma nemi Allah ya saka musu.

A nashi bangaren malamin yayi ikirarin cewa an daura masu aure daidai da koyarwar addini, ana gobe za su yi tafiya amma ba wai fyade yayi bata ba.

“Matata ce ba wai daliba kawai ba. Ta yi rashin hankali ne kuma na fada ma iyayenta cewa bana muradinta kuma iyayen nata na son tursasa ni aurenta. Abunda tayi, bana tunanin akwai wanda zai yarda da hakan. Ta je gidan wani mutum tsawon kwanaki biyu.

“Bayan kwana 15, sai na ga hotunan. Na je ga yan uwanta da mahaifiyarta na nuna masu hotunan. A lokacin ne na bayyana cewa bana muradinta kuma. Tun lokacin suke ta kullamun sharri don na aure ta."

Da aka tambaye shi ko akwai takardu ko hotuna da za su tabbatar da ikirarin cewa sun yi aure, bai gabatar da kowane ba amma ya bayyana cewa yan uwan yarinyar maza su biyu da abokinsa sun shedi auran.

Sai dai yan uwan yarinyar sun karyata batun masaniya kan auren, inda suka bayyana cewa haduwar da suka yi don tattauna batun kin amincewa da auren malamin da yarinyar tayi ne.

A lokacin da aka tuntubi yan sandan jihar Osun, wanda ke rike da laamarin, sun bayyana cewa hukumar tsaro na gudanar da bincike na musamman sannan cewa za su gano bakin zaren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: