Sojoji sun halaka masu garkuwa da mutane 15 a jahar Zamfara
Dakarun rundunar Sojin Najeriya dake gudanar da aikin Operation Hadarin Daji, OPHD, a jahar Zamfara sun bindige wasu gungun yan bindiga su goma sha biyar har lahira a yayin karan batta da suka yi da juna.
Jaridar New Nigerian ta ruwaito mukaddashin kaakakin OPHD, Laftanar Ayobami Onirisan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni, inda yace sun kashe yan bindiga 15, tare da lalata sansanoninsu.
KU KARANTA: Shugabancin majalisa: Akwai jikakkiya tsakanin Ganduje da Oshiomole
“A kokarinmu na kawo karshen ayyukan miyagu yan bindiga, masu garkuwa da mutane da barayin shanu a jahar a Zamfara, dakarun Sojin Najeriya sun yi arangama da yan bindiga, inda aka yi musayar wuta a tsakani, amma daga bisani Sojoji suka samu nasara, har suka kashe yan bindiga 15.
“Bugu da kari Sojojin sun lalata sansanin yan bindiga, tare da kayan aikinsu, yayin da wasu daga cikinsu suka tsere dauke da rauni da suka samu daga samamen.” Inji shi.
A wani labari kuma, Kaakakin yace Sojoji sun kama wasu mutane biyu dake yi ma yan bindiga leken asiri a kauyen Bagega na jahar Zamfara, haka zalika Sojojin sun gano tarin shanu dayawa a kauyen Madada bayan sun fatattaki yan bindiga dake kauyen.
Daga karshe kaakakin ya yi kira ga jama’an yankin dasu dinga taimaka ma Sojoji da bayanan sirri domin hakan zai taimaka wajen bankado duk inda yan bindigan suke tare da kawo karshensu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng