Wata Sabuwa: Ba Almajiranci zamu hana ba, zamu zamanantar da makarantun allo ne - Shugaba Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mutane sunyi masa mummunar fahimta dangane da batun hana almajiranci
- Shugaban kasar wanda yayi magana ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ba almajiranci za a hana ba, kawai za'a yiwa lamarin kwaskwarima ne
- Ya ce za'a zamanantar da harkar ne ba wai za a hana gabatar da almajirancin bane duka, kuma ba wai yanzu zai fara gabatar da hakan ba
Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa mutane da kafafen yada labarai na kasar nan sun yiwa gwamnatin shugaban kasa wata mummunar fahimta akan zancen gyaran da ta bayyana cewa za ta yi akan harkar almajiranci.
A wata hira da Malam Garban yayi da wakilin BBC, Ishaq Khalid, ya bayyana cewa, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana so taga tayi kokari wurin kawo gyara a harkar almajiranci a yankin arewacin Najeriya, inda ta bukaci cewa zata zauna da masu ruwa da tsaki a harkar domin nemo bakin zaren.
KU KARANTA: Dubu ta cika: An kama wani soja da yake sayarwa da 'yan ta'adda makamai a jihar Kaduna
Batun hana almajiranci dai ya kawo kace-nace a wurin 'yan Najeriya a makonnin da suka gabata, inda a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar ya bayyana cewa, shugaban kasar ya sha alwashin kawo karshen almajiranci a kasar nan amma ba kwana kusa ba.
Kafin a fitar da sanarwar sai da shugaban kasar ya maimaita aniyarsa ta cewa yana son ganin dukkanin yaran Najeriya sun samu ilimin da ya kamata, inda ya bayyana cewa zai dauki mataki kwakkwara akan yaran da basa zuwa makaranta.
A kwanakin baya ne dai majalisar dinkin duniya wacce ke kula da asusun yara wato UNICEF, ta ba da sanarwar cewa kimanin yara miliyan takwas ne basa zuwa makaranta a jihohi 10 na Najeriya.
Majalisar ta bayyana cewa yaran duka sun fito daga jihohin arewa ne, irin su:
- Adamawa
- Bauchi
- Gombe
- Kano
- Katsina
- Kebbi
- Niger
- Sokoto
- Taraba
- Zamfara
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng