Shugaban kasa Buhari zai nada kwamiti domin maganin rikicin sassan Najeriya

Shugaban kasa Buhari zai nada kwamiti domin maganin rikicin sassan Najeriya

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya fara shirye-shiryen tattaunawa domin kafa wani babban kwamiti na musamman da zai ja kowa a jiki domin duba rikicin da a ke fama da su a kasar.

Kamar yadda labari ya zo mana, fadar shugaban kasar ta bayyana wannan ne a Ranar 29 ga Watan Yuni, 2019. Fadar shugaban kasar ta ce wannan rikici da a ke ta yi, ba ya yi wa shugaba Buhari dadi.

Malam Garba Shehu, wanda shi ne ke magana da yawun bakin shugaban kasar ya bayyana cewa wannan kwamiti zai yi aiki ne domin kawo shawarwari da su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a Najeriya.

A cewar Garba Shehu, wannan kwamiti na musamman zai duba yadda wadannan rikici da su ka dade su na sanadiyyar asarar dukiya da rayuka, zai zama tarihi. Wannan rikici ya jefa kasar cikin halin dar-dar a yau.

KU KARANTA: Jerin Jihohin Arewa da a ka fi kashe jama'a a shekarar nan

Mai magana da yawun shugaban kasar ya yi magana na musamman a kan rikicin Mutanen Tibi da Jukunnawa da a ke fama da shi a yankin Taraba da jihar Benuwai, inda ya ce za a yi maganin wannan rigimar.

Wannan kwamiti da za a kafa zai kunshi manyan Sarakunan gargajiya da kuma kungiyoyin addini irin su CAN da NSCIA. Kwamitin zai kunshi Matasa da Dattawa da jami’an tsaro da sauran mutanen gari.

A na sa rai cewa wannan kwamiti da zai yi aiki da ofishin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya zai kawo zaman lafiya tsakanin Makiyaya da Manoma da sauran kabilu da masu mabanbantan addinai a Najeriya.

A cewar Kakakin shugaban kasar, banbancin mutanen kasar shi ne karfin su idan har a ka nemi zaman lafiya da aminci. Buhari ya yi kira ga jama’a su kara hakuri da juna a daidai wannan lokaci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel