Zan bada kulawa ta musamman a kan iyakokin Najeriya domin yakar rashawa da ta’addanci, inji Buhari
-Shugaba Buhari ya sake bayyana aniyarsa ta ganin bayan rashawa da kuma ta'addanci a Najeriya
-Shugaban kasar, yayi wannan jawabin wurin wani taro musamman da aka shirya kan lamuran tsaro a babban birnin tarayya, Abuja ranar Juma'a
Shugaba Muhammdu Buhari a ranar Juma’a yayi alqawarin yakar ta’addanci da kuma cin hanci da rashawa har zuwa kan iyakokin Najeriya.
Shugaban ya alkanta cigaba da yaduwar tashe-tashen hankula a duniya a yau da ayyukan cin hanci da rashawa musamman yankin kasashen yammacin Afrika.
KU KARANTA:Sanusi ya tsige Limamin wani masallacin Juma’a
Shugaba Buhari ya yi wannan furucin wurin taron sha’anin tsaro na Munich Security Conference da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a.
Har ila yau, ya kara da cewa, “shige da ficen wasu nau’ukan muggan makamai a Najeriya da kuma sauran kasashen Afirka nada nasaba ne da laifukan rashawa, ta yadda har ta kai manya da kananan makamai na samun shiga kasashe da dama."
Ya cigaba da cewa: “ Yaduwar makamai ta haramtacciyar hanya shi ke kara hura wutar ta’addanci a yakinmu. Hakan kuwa ya samo asali ne a dalilin rashawa da tayi mana katutu a cikin ‘yan shekarun nan.
“ Wannan dalilin ne ya sanya zan cigaba da yakar cin hanci da rashawa da karfin gaske har zuwa kan iyakar Najeriya. Har wa yau, hukumomin da ke da haqqi wurin kare iyakokin kasar, na da bukatar su mike tsaye domin ganin mun kawar da wannnan matsala da ta dade tana ci mana tuwo a kwarya.”
“ Yankin Afirka ta yamma ba a wurin rashawa kawai ya yi kaurin suna ba, hadda bangaren safarar miyagun kwayoyi, safarar mata da kananan yara da kuma garkuwa da bil adama wanda a yanzu ya kamata a ce mun kawar da wadannan matsaloli gaba daya.” A cewar Buhari.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng