Sanusi ya tsige Limamin wani masallacin Juma’a
-Sarkin Kano ya cire babban limamin masallacin Juma'an Limawa
-Sarki Sanusi ya tsige limamin ne sakamakon bijirema umarninsa kan sha'anin ganin watan sallar idi da ya yi har sau biyu
-Limamin da aka ciren dai sunansa Salihu Muhammad wanda kuma yaki cewa komi a kan maganar yayin da 'yan jarida suka nemi jin ta bakinsa
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido na biyu a ranar Juma’a ya bayar da umarnin tsige babban limamin masallacin Juma’an Limawa dake karamar hukumar Kumbotso a jihar, Malam Salihu Muhammad.
Tuni dakatar da wannan limami ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba. Muhammad dai, ana zarginsa ne da sabawa umarnin Sarki a kan ganin watan sallar idi. Abinda wannan limamin ya aikata kuwa shi ne, bai ajiye azumi ranar da aka ga wata ba said a ya kara kwana daya bayan ya ga watan da idonsa sannan ya jagoranci ta shi sallar idin.
KU KARANTA:Duk tsuntsun da ya ja ruwa: Kasar Iran ta gargadi Trump a kan maganar yaqi
Sanusi ya bayyana cewa ba yanzu limamin ya fara wannan dabi’a ba, ko a shekarar da ta gabata ya aikata irin wannan abu.
Haka zalika, ya nuna cewa, tunda har dai limamin ya zama mai kunnen kashi ta hanyar maimaita laifin da aka gargadeshi a kai, to ya zama wajibi a sauya shi da wani daban.
‘Yan jarida sun tuntubi limamin da aka tsigen domin jin ta bakinsa amma abin ya gagara.
A wani labarin mai kama da wannan, mun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi Lamido na II ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda yake bada himma wurin yaki da talauci a kasar nan.
Sarkin yayi wannan jawabin ne wurin wani taro na musamman da aka gudanar a jiharsa ta Kano, a karkashin ofishin babban ma'ajin gwamnatin tarraya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng