Aiki ga mai kare ka: Manyan ayyuka guda 21 da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a yankin Arewa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi aiki masu yawan gaske a yankin arewa, amma mun dan binciko muku kadan daga cikin ayyukan shugaban kasar
A lokuta da dama zaka ji mutane na maganar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yafi yin aiki a yankin kudancin kasar nan.
Hakanne ya sanya Legit.ng ta koma gefe ta tattaro muku wasu manyan ayyuka guda 23 da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a yankin arewaa daga hawan shi mulki zuwa yau.
1. Aikin hanya mafi girma a Najeriya, wacce ta taso daga Kano zuwa Abuja, mai tsawon kilomita 400.
2. Aikin tashar wutar lantarki mafi girma a tarihin Najeriya ta Mambila Hydro Power Station, wacce zata samar da wuta megawatts 3050 idan an kammala.
3. Aikin bincike da kuma hako man fetir a Bauchi da Maiduguri.
4. Tashar jirgin ruwa ta farko a tarihin yankin arewa ta Baro Sea Port dake jihar Niger.
5. Aikin hanyar jihar Kano zuwa jihar Katsina.
6. Aikin hanyar Kano, Bauchi, Potiskum da Borno.
7. Ya mayar da filin jirgin sama na Malam Aminu Kano irin na kasar Turai.
8. Aikin hanyar Bye Pass na jihar Kano.
9. Ya gina Jami'ar sojoji ta Biu a jihar Borno, wacce yanzu haka an fara karatu a cikinta.
10. Ya gama aikin tashar wutar lantarki ta Kashimbila dake jihar Taraba.
KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Na fiso na fito a matsayin fitsararriya a film - Maryam Yahaya
11. Ya kusa kammala gina tashar wutar lantarki ta Zungeru dake jihar Niger, wacce aka watsar da aikin shekara da shekaru.
12. Ya kammala tashar jirgin kasa wacce ta tashi daga Kaduna zuwa Abuja.
13. Shirin ciyar da yara 'yan firamare a jihohin Najeriya.
14. Ya gina Air Force Base mai girma, da babban asibitin sojoji a jihar Bauchi.
15. Shirin N-Power.
16. Shirin tallafin noma da gwamnati take bayarwa kashi 76 na arewa ne.
17. Aikin titin jirgin kasa da ya tashi daga Kaduna zuwa Kano, wanda yanzu ake kan yi.
18. Ginin Commodity Market dake karamar hukumar Gezawa jihar Kano.
19. Ya gina Police Academy Secondary School a kafin Madaki dake jihar Bauchi.
20. Ya bayar da naira miliyan 60 ga jihar Kano domin samar da ruwan sha.
21. Aikin hanyar Ganye, Mayo Belwa, da Toungo mai tsawon kilomita 112, wanda yanzu haka an kusa kammalawa a jihar Adamawa.
Wannan kadan ne daga cikin ayyukan shugaban kasar, wanda yayi a yankin nahiyar arewa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng