Tirkashi: Kayi mini aure ko na shiga karuwanci - Abinda wata budurwa ta gayawa mahaifinta kenan bayan yaki yi mata aure

Tirkashi: Kayi mini aure ko na shiga karuwanci - Abinda wata budurwa ta gayawa mahaifinta kenan bayan yaki yi mata aure

- Babbar matsalace yarinya budurwa ta bukaci mahaifinta yayi mata aure yaki yarda

- Ana samun iyaye wadanda suke da tsattsauran ra'ayi, suce dole sai 'ya'yansu sunyi karatun boko kafin suyi musu aure

- Yanzu wani zamani ne da muke ciki da ba wuya halayen yara ya gurbace, musamman 'ya'ya mata

Akwai babbar matsala ga halayen 'yan mata wadanda suka nemi iyayensu suyi musu aure suka ki. 'Yan mata masu yawan gaske suna shiga harkar karuwanci, shaye-shaye, idan har suka bukaci aure iyayensu suka ki yi musu.

A lokuta da dama 'yan mata na bukatar aure sai iyayensu suki amincewa saboda suna so suyi karatu, ko kuma ta kawo wanda basu so, kuma wani dalili nasu.

KU KARANTA: Yabon gwani ya zama dole: Ayyuka guda 20 da IBB yayi wadanda har yanzu ake cin moriyarsu

Akwai wata yarinya da ta bukaci mahaifinta yayi mata aure, har ta kawo mishi saurayin da take so, amma uban yarinyar yaki yarda, a karshe yarinyar ta rubuta masa wata wasika, inda take cewa: "Na tafi idan ka zo lahira Allah zai yi mana hisabi." Kawai sai ta hau saman bene ta fado ta mutu a take a gurin.

Haka ita ma wata budurwa ta samu mahaifinta akan tana son yayi mata aure ko kuma ta shiga duniya.

Iyaye na da babban kalubale a gaban su, idan aka yi la'akari da irin abubuwan da ke faruwa a wannan lokacin, akan yadda yara ke lalacewa, da kuma wannan sabon bala'in da ya fito na yanzu, wanda haka kawai za a iske mutum ya kashe kanshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng