Jin dadi na inda yake: An ba wa wata jaririya kyautar tikitin jirgi na tsawon shekara 25, saboda an haifeta a cikin jirgi

Jin dadi na inda yake: An ba wa wata jaririya kyautar tikitin jirgi na tsawon shekara 25, saboda an haifeta a cikin jirgi

- An haifi wata jaririya a kasar Ireland a cikin jirgin kasa, yayin da yake tafiya

- Ma'aikatan jirgin sun yiwa jaririyar kyautar tikitin jirgi na tsawon shekaru 25 ba tare da ta biya ko sisi ba

- An samu taimakon wani likita da wata ungozoma ne a cikin fasinjojin jirgin wadanda suka karbi haihuwar matar a lokacin da jirgin ke tafiya

Wata jaririya da aka haifa a kasar Ireland yayin da mahaifiyarta ke tafiya a cikin jirgin kasa, an ba wa jaririyar kyautar tikitin jirgi na tsawon shekara 25 ba tare da ta biya ko sisi ba.

Mahaifiyar jaririyar ta haihu ne, yayin da jirgin yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Dublin inda ya taso daga birnin Galway da misalin karfe 3 na ranar Talatar da ta gabata.

An samu nasarar mahaifiyar ta haihu lafiya ne bayan da aka samu likita da kuma ungozoma a cikin fasinjojin jirgin, wadanda suka taimaka suka karbi haihuwar.

KU KARANTA: Allah Sarki: Yadda 'yan uwana suka dinga cin zarafi na saboda munin da Allah yayi mini - Krepin Diata

An dauki mahaifiyar yarinyar da jaririyar zuwa asibiti bayan sun je birnin Dublin domin duba lafiyarsu, inda kuma aka same su cikin koshin lafiya.

Direban jirgin mai suna Iarnrod Eireann ya bayyana cewa, sun bai wa jaririyar kyautar tikitin shiga jirgi kyauta daga ranar da aka haifeta har zuwa nan da shekaru 25, saboda haifarta da aka yi lokacin da jirgin ke tafiya.

A karshe direban jirgin ya ce: "Muna godiya ga dukkan abokanan huldarmu da suka taimaka wurin karbar haihuwar wannan mata a cikin jirgin nan, mun gode kwarai da gaske."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng