Tashin hankali: Wata mata ta kashe mijinta ta kuma cinna wa gawarsa wuta
Wani ma'abocin amfani da dandalin sada zumunta na Facebook ya yada labarin wata mata da ta kashe mijinta sannan ta saka wa gawarsa wuta bayan sun yi wani kazamin fada.
A cewar wanda ya yada labarin, lamarin ya faru ne a jihar Bayelsa, sannan ya kara da cewa lamarin ya jawo hankalin makwabtan ma'auratan wadanda suka kira 'yan sanda.
Ya kara da cewa, jami'an 'yan sanda sun zo sun dauki gawar mijin sannan sun tafi da matar.
Ko a kwanakin baya sai da wata matar aure ta yi yunkurin kashe mijinta ta Hanyar caka masa wuka a ciki, 'wai' saboda zai kara aure.
Ana zargin wata mata mai suna Amina Banaga Maru dake garin Gusau babban birnin jihar Zamfara da niyar hallaka mijinta ta hanyar soka masa wuka a ciki har sau uku.
DUBA WANNAN: Arziki: TY Danjuma ya sayi Otal din kasar Ingila mai daki 14 da aka gina shekaru 300 da suka gabata a kan biliyan N1
Lamarin wanda ya auku a Litinin, 24 ga watan Yuni, bincike ya nuna cewa matar ta yi niyar halaka mijin nata ne saboda tsantsar kishi.
Bayanan da muka samu sun tabbatar mana da cewa ana zargin Amina ta yi wa mijin nata wannan danyen aikin ne saboda niyyar da yake da ita na yi mata kishiya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng